Illolin wallafa ayyukan baɗala a shafukan sada zumunta

Spread the love

Daga HASSAN IMRAN

A wasu shekarun baya isar da saƙo na ɗaukar dogon lokacin kafin ya isa inda ake so. Hakan ya janyo wahala wajen sada zumunci da kuma isar da saƙon gaggawa. Cigaba da aka samu ta hanyar fasahar zamani ya kawo sauƙi a ciki rayuwar ɗan’adam. Daga cikin sauƙin da aka samu shi ne fitowar manhajoji a kafafen sadarwar zamani. Daga cikin irin waɗannan kafafen sada zumunta da aka fi amfani da su akwai irin su Facebook, Instagram, ɗ, WhatsApp, Snapchat, Tik Tok da sauran su.

Waɗannan shafukan sada zumunci ana amfani da su ta hanyoyi da yawa. Daga ciki, ana tura saƙonni, ana hira da abokan arziƙi, ana ilimantar da kuma wayarwa al’umma kawuna. Harwayau, ana shirya tattaunawa tsakanin juna da kuma tallace-tallacen abubuwan kasuwanci da sauran su.

Mun wayi gari a yau, wani bala’i ta ya kunno kai wanda ke neman zama kamar wata al’ada a cikin bi’ar mu. Babu shakka ya zama ruwan dare musamman a tsakanin matasan mu. Wannan bala’i kuwa shi ne bayyana tsiraici da abubuwa na rashin dacewa a fili da matasan Arewa ke aikata wa ta manhajojin sada zumunta. Bayyana zunubi a fili shi ne tattauna zunubi da mutum ya aikata ko kuwa zai aikata ta hanyar gayawa wani ko kuwa wallafa hoto ko bidiyon abin da ya aikata a shafukan sada zumunta. Daga cikin shafukan da matasa Arewa ke amfani da su ta hanya da bata dace ba akwai irinsu Facebook, Instagram da kuma Tik Tok. Suna yaɗa munanan ɗabi’u marassa kyau a yanar gizo.

Munanan ayyuka da kuma rashin kunya da matasan Arewa musulmai suke aikatawa musamman ta manhajar Tik Tok yayi matukar muni. Tik Tok wata manhajar waya ce wacce take ba da dama ga masu ta’amuli da ita su ƙirƙiri wani  ƙaramin bidiyo na nishatarwa ko kuma wallafa bidiyo akai. Wannan bidiyo ba ya wuce minti talatin ba ko daƙiƙa uku. Mafi yawan masu mu’amala da Tik Tok suna amfani da shi ne wajen ƙirƙirar bidiyon batsa kamar rawar baɗala da ‘yan matan Arewa ke yawan yi akai, furucin batsa ko kuma shirya wani taron batsa inda ake tattaunawa maganganu banza tsakanin ‘yan mata da gurɓatattun matasan Arewa Musulmi. 

Abin haushi shi ne, idan ka shiga manhajar Tik Tok kafin ka ga wani bidiyo na wa’azi ko kuwa nasiha sai ka ci karo da bidiyoyin batsa waɗanda ke nuna tsiraicin mata da kuma rawar rashin kunya da wasu matan ke yi, wanda ke nuna wasu gaɓoɓin da bai halasta a gani ba face ga muharaminsu. Da yawa daga cikin matasa maza da mata na wannan shegantaka ne domin neman suna ko kuwa domin neman kuɗi ta hanyar taya wasu masana’ta ko kamfani da shafin su domin tallace – tallace-tallacen kayansu ta hanyar rawa ko kuma yin shigar da bata dace ba, da nufin jan hankalin mutane akan kayan da suke talle a kai.

Haka zalika da yawa daga cikin matasa wanda aka fi sani suna da ‘yan bangar siyasa ko kuma ‘karnuka ‘yan siyasa’ suna amfani da shafukansu wajan zage-zage, tuhume-tuhume da cin mutuncin mutanen da ra’ayin siyasar su ya bambanta da na ‘iyayen gidansu na siyasa. Harwayau, wasu matasa na amfani da shafukansu wajen zagi da cin mutuncin malaman addinin musulunci da akidarsu ko fahimtarsu ta bambanta. Wannan halin ya ƙara hura wutar rashin kunya a zukatan wasu matasan Arewa.

A makon da ta gabata wasu jaridun turanci na The Punch da Tribune sun rawaito wani labarin takaici a yayin da wani matashi mai shekara ashirin da hudu a garin Kano ya sa wani abokin sa yayi bidiyonsa yayin da ya riƙe wata akuya yana tsotsan farjin ta. Wannan bidiyon ya watsu a Tik Tok ta inda kowa ya gani sai ya yi Allah wadai da irin wannan halin. Hukumar Hisba ta jihar ta yi ƙoƙari wajen gano inda matashin yake da kama shi, wanda a lokacin da ake tambayar sa kan me ya sa ya aikata haka?  Sai ya amsa masu cewa yana so ya yi suna ne kowa ya san shi, shi ya sa ya aikata haka. To, wannan masifar da mai ta yi kama?

A yayin da matasan mu ke amfani da shafukan sada zumunta ta hanyar da bata dace ba wasu matasa a wasu yankuna na amfani da wannan damar ne wajen ƙara wa junansu ilimi da kuma koyon sana’o’in zamani kamar su ilimin zane da koyarwa, binciken bayanai, tallace-tallace na zamani akan shafukan sada zumunta da sauransu. A ƙasar China, sun fitar da wani sabon tsari na koyawa yara yadda ake amfani da fasahar zamani ta Artificial Intelligence (AI) daga matakin firamare har zuwa matakin sakandire. Mu kuma namu a nan sun mayar da hankali kan rawar banza ne kamar wata hanyar cigaba.

Lallai ne mu sani cewa bayyana zunubi a shafukan sada zumunta na da illoli ga ma’abota da kuma rayuwar su. Yana hargitsa sha’anin tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma, kuma yana gurɓata halayyar matasa ta hanyar hulɗa da ɓatagari. Haka zalika, yana janyo annoba da kuma fushin Ubangiji. Ma’aikin Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya yi mana gargaɗi kan cewa, ‘Babu yadda alfasha za ta bayyana a cikin mutane ta hanyar da za su bayyana zunubi a fili facce Ubangiji Ya jarabce su da cututtuka da annoba wanda mutanen da suka gabace su basu san da su ba.’ Har wayau, bayyana zunubi a fili na hana addu’ar al’umma karɓuwa.

Iyaye, ya zama dole su kula da abubuwan da ‘yan’yansu ke aikatawa a shafukan sada zumunta. Su sani wannan haƙƙinsu ne, kuma Allah zai tambaye su a kai. Matasa masu yaɗa fitsara da alfasha a shafukan sada zumunta su tuba zuwa ga Allah daga wannan aikin saɓo da suke aikatawa, kuma su sani cewa duk abinda suka wallafa a shafinsu yana da tasiri ko ya haɗa kawunan al’umma ya kawo cigaba a cikin su, ko kuwa ya kawo rabuwar kawuna da rashin yarda da juna. Matasa su ji tsoron Allah a dukkan harkokinsu akan shafukansu na sada zumunta sun sani cewa za su yi wa Allah bayani akan abubuwan da suke aikatawa. Malamai su zurfafa wajen karantar da al’umma musamman matasa kyawawan ɗabi’u da kuma jan hankalin su daga ayyukan sabon Allah. Ma’aikata masu kula da sadarwa su taimakawa wajen kawo dokoki masu tsauri da za su hana wallafa baɗala a shafukan sada zumunta.

Allah Ya taƙaita mana masifu Ya kuma shige mana gaba a harkokin mu. Allah Ya shirya mana matasan mu maza da mata, Ya zaunar da ƙasar mu lafiya. Amin. 
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected]

By ukarofi