Imisi ta lashe gasar BBNaija zango na 10

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Lahadi Imisi Ayanwale ta zama gwarzuwa a gasar Big Brother Naija a zango na 10, lamarin da ya sa ta samu kyautar Naira miliyan 150.

Hakan ya biyo bayan watanni ana gudanar da wasa mai ɗauke da nishaɗi, barƙwanci da lokuta masu ɗebe kewa.

Ayanwale ta samu goyon baya daga tawagar masoyanta da aka sani da ‘Ijoba 606’, wanda hakan ya sa ta doke manyan abokan karawarta ciki har da Dede da ake kira da Koyin, Kola, Isabella da Kaybobo a matsayin na biyu.

Duba da ƙwarewarta ta fuskar iya sarrafa harshe da nishaɗantarwa, hakan ya sa ta zama tauraruwa a gidan da ake gabatar da shirin musamman ganin yadda ta ke ƙoƙari wajen fuskantar ƙalubale.

Shirin BBNaija yana ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ke ɗauke hankalin masu kallo musamman ganin yadda ake yawan ajiye su cikin jiran tsammani na abinda ka iya zuwa daga baya.

Waɗanda suka taɓa lashe gasar a baya sun haɗa da Mercy Eke, Laycon, Whitemoney, Phyna, Ilebaye da sauran su.

By Babaji