
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da biyan kimanin Naira biliyan N2.321 domin sauke haƙƙoƙin fansho, kuɗin sallama da kuma tallafin mutuwa ga tsofaffin ma’aikata da iyalan waɗanda suka rasu a bakin aiki a jihar.
Rabon kuɗin wanda yake karkashin tsarin fansho na haɗin-gwiwa (CPS) da kuma biyan kudin barin aiki dana mutuwa karkashin tsohon tsarin biyan kudin inda , gwamnatin Kaduna ta riga ta biya jimillar naira ₦6.678bn a shekarar 2025, da kuma jimillar ₦13.5bn cikin shekaru biyu na wannan gwamnatin mai ci.
A wata sanarwar manema labarai wanda Kwamishinan Ma’aikatar yada labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya rabawa manema labarai yace kula da jin daɗin tsofaffin ma’aikata na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci, tare da tabbatar da biyan hakkokin su a kai a kai domin rage musu radadin rayuwa.
Maiyaƙi ya ce Gwamna Uba Sani ya sha jaddada cewa, tabbatar da mutunci da jin daɗin tsofaffin ma’aikata ba kawai nauyin doka ba ne, har ma ɗabi’a ne da gwamnati ke ɗauka da muhimmanci.
A cewar Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna, Ibrahim Balarabe, yace sabon rukuni na biyan kudi zai amfanar da tsofaffin ma’aikata 661 da iyalan waɗanda suka rasu a matakan Gwamnatin Jiha da ta Kananan Hukumomi naira biliyan 1.736 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 511 ƙarƙashin tsarin ( CPS) sannan kuma naira miliyan 585 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 315 da iyalan mamata karkashin tsarin (DBS)
Hukumar ta bayyana cewa, ga waɗanda ke karkashin fanshon hadin gwiwa na (CPS), hakkokin su za a tura kai tsaye cikin asusun fansho (Retirement Savings Accounts – RSAs) ɗin su, yayin da waɗanda ke karkashin tsarin (DBS) za a gayyace su nan gaba don yin tantancewa kafin a biya su.
A ƙarshe, sanarwar ta bayyana cewa wannan amincewa ta sake tabbatar da jajircewar gwamnatin jihar wajen kare rayuwar tsofaffin ma’aikata, tabbatar da hakkokinsu, da kuma ƙarfafa amincewar ma’aikatan Kaduna da gwamnati.
