
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Maitaimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a jamm’iyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar ya bayyana nadamarsa akan kasancewa cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2014 domin kayar da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
Atiku ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai da jagororin adawa suka shirya a Abuja, ranar Alhamis.
A cewarsa, dalilin haɗuwar manyan ’yan siyasa a wancan lokaci shine samar da sauyi a shugabanci da inganta rayuwar al’umma.
Saidai ya yi ikirarin cewa halin da ƙasar ke ciki a yanzu ya fi muni a ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu idan an kwatanta da wancan lokacin.
Kalmar nadamar na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da muhawara kan tattalin arziƙi, tsaro da sauran manyan ƙalubalen da ke gaban gwamnati.
Masu goyon bayan gwamnatin na cewa ana aiwatar da sauye-sauye masu tsauri da za su haifar da ɗa mai ido a gaba, yayin da masu suka ke ganin sakamakon bai kai yadda aka yi alkawari ba.
Wannan batu ya sake tayar da zazzafar muhawara akan tasirin sauyin mulki da kuma ko manufofin da aka ɗora wa jam’iyyar a lokacin kafuwarta sun cimma burinsu ko kuma akasin haka.
