Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin ƙasa ta ƙaddamar da gagarumin sauyi a tsarin zaɓen Nijeriya bayan amincewa da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ta tanadi ɗaurin shekara biyu ba tare da zaɓin tara ba ga duk wani Kwamishinan Zaɓe na Jiha (REC) da ya ƙi fitar da muhimman takardun zaɓe, tare da kafa asusun musamman domin tabbatar da cikakken ’yancin kuɗi ga INEC gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ne ya bayyana muhimman tanade-tanaden dokar a Abuja, yana mai cewa an kwashe kusan shekaru biyu ana nazari da tattaunawa kafin a cimma matsaya kan gyaran tsarin zaɓen ƙasar.
Sabuwar dokar ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke sukar wasu sassa na tanade-tanadenta, musamman waɗanda suka shafi zaɓukan fidda gwani, iyakar kuɗin yaƙin neman zaɓe da jadawalin zaɓe.
Sai dai ɓangaren gwamnati da jam’iyyar APC sun kare dokar, suna mai cewa gyare-gyaren sun dace da buƙatar zurfafa dimokuraɗiyya.
Sashe na 74(1) na dokar ya wajabta wa REC fitar da sahihin kwafin duk wata takardar zaɓe cikin sa’o’i 24 bayan an biya kuɗin da ya dace. Duk wanda ya saɓa wa hakan zai fuskanci aƙalla ɗaurin shekara biyu ba tare da zaɓin tara ba. ‘Yan majalisa sun ce hakan zai kawo ƙarshen ƙin bada takardu da ke haddasa zargin maguɗi.
Haka kuma, Sashe na 72(2) ya ba da damar amfani da sahihin kwafin umarnin kotu wajen rantsar da wanda kotu ta tabbatar a matsayin wanda ya yi nasara, idan INEC ta ƙi bayar da takardar shaidar cin zaɓe.
A wani mataki mai ƙarfi, Sashe na 3 ya kafa asusun musamman domin tabbatar da cikakken ‘yancin kuɗi ga INEC, tare da tanadin cewa dole ne a saki kuɗaɗen zabe aƙalla watanni shida kafin babban zaɓe.
Sashe na 60(3) ya wajabta tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki zuwa IReɓ, yayin da Sashe na 60(6) ya tanadi ɗaurin watanni shida ko tara N500,000 ko duka biyun ga duk wani jami’in zaɓe da ya hana tura sakamako ta lantarki da gangan.
Sai dai dokar ta ba da damar amfani da fom EC8A idan matsalar sadarwa ta hana tura sakamako, bisa ƙa’idojin INEC.
Sashe na 125 ya ƙara tsaurara hukunci kan sayen ƙuri’u, kwaikwayon masu kaɗa ƙuri’a da sauya sakamako, inda aka tanadi ɗaurin shekara biyu ko tara daga N500,000 zuwa N2 miliyan ko duka biyun.
Dokar ta kuma ƙara iyakar kuɗin yaƙin neman zaɓe: kujerar Shugaban ƙasa daga biliyan N5 zuwa N10 biliyan; gwamna daga N1 biliyan zuwa N3 biliyan; Sanata daga N500 miliyan zuwa N1 biliyan; dan majalisar wakilai daga N70 miliyan zuwa N250 miliyan; ɗan majalisar jiha daga N30 miliyan zuwa N100 miliyan.
Jam’iyyar da ta gaza gabatar da cikakken rahoton kuɗinta cikin lokaci za ta fuskanci tara N10 miliyan.
Sashe na 84 ya soke zaɓukan fidda gwani na wakilai (indirect primaries), ya bar kai-tsaye da na maslaha (consensus) kawai, domin rage cinikin ƙuri’un wakilai da kara buɗe dama ga mambobi.
Hakazalika, Sashe na 77 ya wajabta wa jam’iyyu su mallaki rijistar mambobi ta dijital tare da mikawa INEC kwafin rijistar aƙalla kwanaki 21 kafin taruka ko zaɓukan fidda gwani. Duk jam’iyyar da ta saba ba za ta samu damar tsayar da ‘yan takara ba.
An daidaita ƙudirin tsakanin majalisun biyu kafin a aika wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya rattaba hannu cikin sa’o’i 24 da wucewar ƙudirin. Duk da cewa wasu kungiyoyin fararen hula sun nuna damuwa kan saurin amincewar, shugabannin majalisa sun ce an yi cikakken tuntuba da hukumomi da ƙungiyoyi daban-daban.
A cewar Bamidele, sabuwar dokar ta zo ne domin ƙarfafa gaskiya, rage taƙaddamar zaɓe da kuma tabbatar da cewa tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya ya samu ingantacciyar kafa.
