Dangote ya bayyana lokacin fara sayar da hannun jarin matatarsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa cikin watanni huɗu zuwa biyar masu zuwa, za a bai wa ’yan Nijeriya damar sayen hannun jari kai tsaye a matatar man fetur ta Dangote, wani mataki da ake kallonsa a matsayin sabon babi a tarihin zuba jari a ɓangaren mai na ƙasar.

Dangote ya yi wannan bayani ne yayin wata ziyara da Shugaban Rukunin Kamfanin Man Fetur na ƙasa, Bayo Ojulari, ya kai matatar tare da tawagar manyan jami’an gudanarwa na NNPC.

A cewarsa, NNPC na riƙe da kaso 7.25 cikin ɗari na hannun jarin matatar a madadin ’yan Nijeriya, yana mai cewa wannan kaso ya fi na wasu manyan masu hannun jari a wasu kamfanoni na duniya.

Ya jaddada cewa ba da jimawa ba, kowane ɗan Nijeriya zai samu damar mallakar kaso a wannan babban aiki na ƙasa.

Dangote ya ƙara da cewa, masu hannun jari za su samu zabin karbar ribarsu ko dai a naira ko kuma a dalar Amurka, ganin cewa matatar na samun kuɗin shiga a kasuwannin waje.

Wannan, a cewarsa, zai ƙara jan hankalin masu zuba jari tare da bunƙasa haɗin kan ’yan ƙasa a harkar masana’antu.

Ya bayyana ranar ziyarar a matsayin ɗaya daga cikin mafi muhimmanci a tarihin matatar, yana mai cewa NNPC ba baƙo ba ne a wurin, domin su ma masu hannun jari ne tun daga lokacin da aikin ke kan kafuwa.

Dangote ya yaba da irin kwarin gwiwar da kamfanin ya nuna tun a farkon aikin, yana mai cewa sabuwar alaƙar aiki da shugabannin NNPC na yanzu za ta wara faɗaɗa haɗin gwiwa a ɓangaren mai da sauran sassan masana’antu.

Game da makomar haɗin gwiwa, Dangote ya ce ana duba yiwuwar ƙara zurfafa hulɗa a wasu rijiyoyin mai kamar Block 71 da 72, tare da yiwuwar haɗin gwiwa a ɓangaren hakowa da samar da ɗƙnyen mai.

Baya ga tace mai, ya bayyana cewa matatar ta zama cibiyar masana’antu, inda ake samar da sinadarin linear alkaline benzene, wani muhimmin kayan haɗin sabulun wanki.

A cewarsa, an shirya samar da tan 400,000 na wannan sinadari a duk shekara, adadin da zai wadatar da duk nahiyar Afirka, la’akari da cewa ƙasashen Aljeriya da Masar na samar da ƙasa da rabin wannan adadi a halin yanzu.

Matatar da ta kai darajar dala biliyan 20 ta fara aiki a watan Janairun 2024, tana da ƙarfin tace ganga 650,000 na mai a rana, tare da samar da kayayyaki kamar jet fuel da naphtha. Masu sharhi na ganin buɗe ƙofar sayen hannun jari ga ’yan ƙasa zai ƙara zurfafa haɗin kai da kuma mallakar tattalin arzikin ƙasa ta hannun jama’a.

By ukarofi