Ina mamakin yawaitar mutuwar auren jarumai mata – Pete Edochie

Daga AISHA ASAS

Shahararren jarumin da ya ga jiya, ya ga yau, Pete Edochie, ya bayyana kaɗuwarsa kan yadda auren jarumai mata ke mutuwa ba ƙyaƙyautawa.

Jarumin ya yi wannan ƙorafin ne a wata tattaunawa da ya yi a shirin nan na ‘WithChude’, inda ya bada misali da auren jaruma Chioma Akpotha, jaruma Ireti Doyle da kuma jaruma Tonto Dikeh, waɗanda igiyoyin aurensu suka tsinke.

“Idan ka je masana’antarmu a yanzu, za ka tarar mafi yawan matanmu da suka yi aure a shekaru biyu zuwa uku baya, auren ya mutu. Na kuma yi matuƙar kaɗuwa da jin mutuwar auren Chioma Chukwuka, Ireti Doyle, da kuma Tonto “inji shi.

Dattijon jarumin mai shekaru 76, ya ce, mata da yawa, ruɗin zuciya da ke nuna masu waje ya fi cikin gidansu daɗi ne ke kai su ga rabuwa da mazajensu, wanda ya bayyana haka a matsayin babban kuskure.

Edochie ya yi kira ga mata da su ɗauki haƙƙoƙin aure da muhimmanci, su jure, su yi haƙuri, su zauna gidajen mazajensu duk wuya, duk daɗi.

Sannan ya musanta cewa, mace da namiji ɗaya ne a zantawarta aure, kuma ya ce, “ba al’adunmu ba ne, namiji ya duƙa bisa gwiwa don sa wa mace zoben aure.”

“Ku tuna cewa, kuna alƙawari kafin aure na ‘a cikin daɗi ko wuya’ ba wai na ‘a cikin daɗin da ya yi mana’ ba.

“Babbar matsalar dai ita ce, kuna sa wa ranku cewa, jin daɗin da yake waje, ya fi wanda yake gidajenku yawa. Wannan shi ne kuskuren da muke yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *