Sai bayan mutuwar babana da aurena ne na samu aka bar ni yin harkar fim – Ummi Tarore

“Har yanzu Ina fuskantar ƙalubale a harkar fim”

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Aisha Adam Muhammad da aka fi sani da Ummi Tarore wata matshiyar da ta ke tashe a masana’artar fim ta Kannywood, a tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da kuma yadda a ƙasa da shekaru biyu ta yi finafinai fiye da 25. Ku biyo mu don jin yadda hirar za ta kasance:

MANHAJA: Gabatar mana da kanki.

UMMI TARORE: Sunana Aisha Adam Muhammad da aka fi sani da Ummi Tarore, an haife ni a shekarar 2002 a Jos, amma a Kano muke zaune. Na yi primary a Mahmud Sani Madakin gini, na yi sakandire a Ammy day Secondary School, dukka a Kano, kuma daga sakandire na tsaya.

Me ya ba ki sha’awa kika shiga harkar fim?

Ina sha’awar fim tun ina ƙarama, amma da yake ban samu goyon baya ba daga iyayena, har na yi aure, to bayan aurena ya mutu, sai babana ya rasu, to shi ne na cigaba da muna sha’awata a fim shi ne babata ta bani goyon baya.

A wacce shekarar kika shiga masana’antar Kannywood?

Na shiga Kannywood a shekarar 2021, kuma na fara da fim mai suna ‘Ashfat’, wanda kuma ni na jagorance shi. Kuma fim ɗin na Alasan Kwalli ne.

A me kika fito a fim din?

Ni ce jarumar fim ɗin, kuma ni na jagoranci fim ɗin, kuma shi ne fim ɗina na farko, ka ga ai na shigo a ƙafar dama.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa kika yi?

Ya zuwa yanzu gaskiya na yi finafinai sun kai guda 25.

Daga cikin finafinan da kika yi wanne ya fi kwanta maki?

Gaskiya fim ɗin ‘Jinin jikina’ shi ya fi kwanta min a rai, saboda a lokacin ɗaukar fim ɗin ba ni ce jarumar fim ɗin ba, amma yanayin ‘acting’ ɗin da na yi ya sa a ka bani bani jarumar fim cin. Don haka to yanayin taka rawar da na yi ita ce ta ke burge ni gaskiya.

Me ya baki sha’awa kika shiga fim?

Akwai wata Zahra Preety da suke yawan yin aiki da MM Sidi, to ‘acting’ ɗin ta yana burgeni sosai, musamman idan ta fito a masifaffiya tana faɗa da mijinta, to sai na riƙa jin daɗi, sai na riƙa jin ina ma ni ce, idan an vata min rai da na kalla sai na ji nishaɗi.

Kin taɓa yin aure?

A yanzu ba ni da aure, amma na taɗa yin aure a 2018, kuma ina da ƴaya biyu mata.

Ta hannun wa kika shiga Kannywood?

Ta hannun MM Sidi na shiga masana’antar Kannywood, shi ne da zan shigo ya yi min nasiha akan na kama kaina na nutsu, daga nan sai ya turani wajen Alasan Kwalli shugaban ‘yan wasa inda na fara fim ɗina na farko.

A lokacin da kika shiga Kannywood kin samu ƙalubale ne ko a cikin sauƙi kika shiga?

Gaskiya na fuskanci qalubale da dama, kuma ina kan fuskanta a halin da ake ciki yanzu. Domin yan’uwana da sauran mutane suna jifa na da maganganu waɗanda ba su dace ba, in taƙaice maka zance mahaifiyata ce kawai da qaninta mai suna Hassan su ne kaɗai suke goya min baya, amma ƴanuwa da ‘yan unguwa ba sa faɗin kalamai na kirki a kaina, kai wasu har karuwa wasu su ce babu inda zanje a fim.

A cikin finafinanki wanne ya fi baki wahala?

Akwai wani fim mai suna ‘Takobin So’ na sha wahala sosai a cikin fim ɗin, domin duk abinda na yi a ciki da gaske na yi, saboda ka ga an sa ni gudu akan dutse, na faɗi na jijji ciwo, anyi garkuwa da ni, kai har rashin lafiya na yi, amma har yanzu ba a saki fim ɗin ba.

Wane ne kuma a finafinanki wanda idan kika tuna shi yake ba ki dariya?

Akwai wani fim ‘Bugun Numfashi’ idan na tuna shi ya na bani dariya gaskiya, fim ɗin na soyayya ne, a lokacin da ake ɗaukar shirin sai na ke jin soyayyar sa a zuciyata, to zarar an ɗauke soyayyar sai na ji babu ita, to shi ne sai abin ya rinƙa bani dariya.

Daga lokacin da kika shiga harkar zuwa yanzu waɗannan irin nasarorori za ki iya cewa kin samu?

Gaskiya na samu nasarori masu yawa, na farko na samu ilimin zamantakewa da mutane , domin ni mace ce mai fushi da saurin hasala, amma shiga ta Kannywood na gane cewa mu’amala da mutane dole sai an yi haƙuri, Alhamdullahi wannan ne fushin yanzu ya sauka. Don haka ni babbar nasarar da na samu ita ce na daina hasala.

Don haka ni babbar nasarar da na samu shi ne, haƙuri da na samu a Kannywood, ni yanzu haka na zama mace mai haƙuri.

Za mu ci gaba.