Gwamnati ta sake maka Emefiele a kotu kan zargin laifuffuka 20

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta sake maka tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele a kotu inda take tuhumarsa da aikata laifuka 20.

Wannan na zuwa ne bayan shigar da buƙatar janye ƙarar “mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya” da gwamnatin ta shigar da fari kan Emefiele ɗin a Babban Kotun da ke zamanta a Legas.

Daraktan sashen shigar da ƙararraki (DPP) a Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa, Mohammed Abubakar, ya sahaida wa alƙalin kotun, Nicholas Oweibo, cewar buƙatar janye ƙarar daga ɓangaren gwamnati ta taso ne domin ba da damar zurfafa bincike.

Sai dai lauya mai kare Emefiele, Joseph Daudu, SAN, ya ƙi amincewa da da buƙatar janye ƙarar da gwamnati ta gabatar wa kotun, yana mai cewa dole gwamnati ta wanke kanta daga rashin ɗa’ar da ta nuna ga umarnin kotun dangane da belin Emefiele kafin a amince da buƙatar tata.

Idan za a iya tunawa, a ranar 25 ga Yuli kotun ta ba da belin Emefiele a kan Naira miliyan 20 kan zargin laifuka biyu da suka haɗa da mallakar bindiga da alburusai ba bisa ƙa’ida ba inda ta ba da umarnin a kai Emefiele a jiye a gidan yarin Ikoyi zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan belin nasa.

Amma daga bisani hukumar DSS ta sake tsare shi bayan da aka tara ‘yan kallo tsakanin jami’an DSS da na gidan yari a harabar Kotun.

Majiyarmu ta tattaro cewa, tuni gwamnati ta sake maka Emefiele a kotu a Abuja kan zarge-zarge guda 20.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske bayan zaman shari’ar da kotu ta yi a ranar Talata, Abubakar ya ce an shigar da sabuwar ƙarar ce a Babbar Kotu mai zamanta a Abuja.

Daga cikin sabbin zarge-zargen da ake yi wa Emefiele ɗin har da amfani da haramtattun damammaki.

A watan Yulin da ya gabata Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele daga ofis.