‘Yan bindiga sun kashe ango da amarya a Filato

Daga WAKILINMU

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wasu ma’aurata da suka yi aure ba da daɗewa ba a Jihar Filato.

Amarya da angon sun cim ma ajali ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari a makarantar BECO Comprehensive High School, da ke Kwi cikin Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Kazalika, an ce maharan sun ji wa wasu da dama rauni, ciki har da mataimakin shugaban makarantar.

Majiyarmu ta ce an kai harin ne a lokacin da malaman makarantar ke tsaka da tattauna yadda za su gudanar da bikin raba kyaututtuka ga ɗaliban makarantar da suka yi fice a zangon karatu mai ƙarewa.

Majiyar ta ƙara da cewa marigayan na aikin koyarwa ne a nan makarantar da harin ya auku.

Bayanai sun ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 3 na rana a ranar Litinin da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *