Shawara game da samun maslaha tsakanin surukai

Tare Da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a kan dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai. Ta yadda surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana.

A wani lokaci a baya mun kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi alƙalanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci gaba da kwararo muku bayani a kan wasu dalilai da suke jawo hakan da ma neman mafita. A sha karatu lafiya.

Wasu ƙarin dalilan da suke jawo surukuta ta taɓarɓare bayan waɗanda muka kawo a baya sun haɗa da:

Kwaɗayi. Hausawa kan ce wai kwaɗayi mabuɗin wahala. Kuma wanda ya hau motar kwaɗayi, to kuwa zai sauka a tashar wulaƙanci. Wato duk yadda aka duba dai sakamakon kwaɗayi ba alkhairi ba ne.

Ma’aurata suna duba wajen maiƙo-maiƙo yayin neman aure. Yadda maza suke, haka iyayen yara mata ma, sammakal. Sai ka ga namiji ba shi da tarbiyya kuma iyayen yarinyar sun san da haka. Amma don yana da hannu da shuni sai ka ga an ɗauki aure an ba shi.

To kuma da ma yaushe zai girmama iyayen mace wato surukansa? Sai ka ga wani ko gaishe da iyayen matar ma wuya yake masa saboda ya raina musu ajawali. Musamman idan ya kula makwaɗaita ne. Sai ya yi ta wulaqanta su. Yana yi musu kyaututtukan da ba su taka kara sun karya ba.

Su ma fa ɓangaren maza ana samun makwaɗaita waɗanda suke da burin auren ‘ya’yan masu hali. Shi ma yawanci a gidan yarinyar sai a dinga raina musu ƙura. Ka ga ko da wajen neman auren komai ya kawo, sai raina masa. Ko idan ta haihu ta zo wankan gida, shi ma haka. Idan mai fushi ne, sai ka ga ya ƙullaci iyayenta kuma ya daina ganin girmansu.

Abinda mutane suka kasa fahima shi ne, ita fa gabar tsakanin suruka da uwar miji ko ‘yanuwansa tun a neman aure ake assasa ta kuma ta ci gaba da addabar zaman auren. Don haka sai a kula.

Dalili na gaba, rashin ƙaunar juna saboda Allah. Kamar yadda Hausawa kan ce, so hana ganin laifi. Haka ma ƙiyayya take rufe idon mutum ta hana shi ganin kirkin wanda ba sa ƙauna. Don haka, su ma surukai hakan tana faruwa da su. Idan suruki ko suruka suna son surukarsu ko me ta yi a wajensu ba laifi. Amma idan ba sa son ta ko ruwa ta taka za a ce ta ta da ƙura. Dole sai an san yadda aka yi aka zaƙulo wani laifi aka manna mata shi. Iyayen miji su suka fi yin haka, musamman ma mata.

Kuma musamman idan ba zaɓinsu ɗan ya bi wajen auro matar ba. Sai ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata. Wani zubin ma duk da yaran da ta haifa jikoki ne ga surukar su ma sai ƙiyayyar uwar ta shafe su idan ba sa’a aka yi ba.

Wani dalilin kuma shi ne, munafunci da tsaigumi. Akwai mutane masu burin tayar da zaune tsaye. Wato su dai ba su da buri sai dai su ga an haɗa waje. Waɗannan mutane haka kawai suna yin irin haka ballantana suna ƙin mutum. Shi munafunci idan ba a yi da gaske ba, ba irin alaƙar da ba ya rusawa. Ko da kuwa ta tsakanin mata da miji ce. Aure ya sha mutuwa saboda munafunci da rashin fahimta.

Haka ma alaƙar surukai. Munafunci yana sanyawa ta yi tsami matuƙa. Yawanci masu kai kawon yaɗa labarai na ta da tarzoma na gaskiya da na ƙarya tsakanin surukai ba sa wuce ƙanne ko yayyen miji. Waɗannan bayin Allah matuƙar ba sa son matar ɗanuwansu, ko kuma ba ta yi musu yadda suke so, to lallai ta gamu da tuggu kala-kala sai dai Allah ya kiyaye ta.

Domin da gaskiya da ƙarya zuwa za a yi a gaya wa iyayen miji. Kuma ba labarin kaɗai za a kawo musu ba. Har da haɗi da zuga. Za a nuna musu cewa ai matar ɗansu ta mallake shi kuma a kamata su maganta abin. Idan ba a samu tsayayyun iyayen miji ba, haka za su faɗa tarkon wannan huɗuba. Kuma sai alaƙar ta ƙi daɗi tsakaninsu da matan ‘ya’yansu.

Akwai kuma faɗar laifin juna wajen iyaye. Kamar yadda Bahaushe yakan ce zo mu zauna, zo mu sava. Haka ma ma’aurata rayuwarsu tamkar kurva ne daga kuttun zuma gauraye da maɗaci. Akan yi daɗin. Haka ma idan saɓanin ya zo akan saɓa. Wani zubin ma a yi kaca-kaca. Amma da yake mata da miji sai Allah, sai ka ga an dawo an ɗinke kamar ba a yi ba.

To inda matsalar take shi ne, idan aka sanar da iyaye wasu abubuwan da aka yi na ɓacin rai, su iyayen ba sa iya mantawa ko da kuwa su ma’auratan sun manta kuma sun yafe wa juna. Amma su iyayen matar kullum kallon surukin nasu suke yi da wancan halin.

Haka shi ma mijin a nasa ɓangaren kullum iyayensa kallon matarsa suke da wannan halin. Ba za su iya yafe mata ba ko da shi ɗan nasu ya yafe mata sun shirya. Kuma daga haka alaqar surukan idan ba wani ikon Allah ba, ta taɓarɓare kenan.

Sannan akwai ramuwa. Akwai wani lokaci da idan aka samu namiji mara kyautata wa surukansa. Wani lokacin ma har iyayen matar yakan kamaya zage su tas kai ka ce ya samu zogale.

Irin haka idan ta ci gaba, ita ma matar takan fusata har ta kai bango ita ma ta daina kyautata wa iyayensa shi ma. Domin za ta ga ai iyaye ba su fi iyaye ba. Don haka ita ma sai ta shiga cin zarafin nasa iyayen.

Sai kuma rashin kyautatawa. Haƙiƙa kyautatawa tana ƙara ingancin kowacce irin alaƙa. Kamar yadda rashin kyautatawar kan rusa alaƙa. Dan Adam yana son mai kyautata masa kamar yadda ya zo a hadisin Annabi (SAW) cewa, Zuciya tana da halayya guda biyu; son mai kyautata mata, da ƙin mai munana mata.

Rashin kyautata wa surukai da cutar da su walau iyayen mijin ko matar ɗa, yana sanya ƙiyayyar mai yi a zuciyar wanda ake cutarwar. Kuma dafin ƙiyayya yana da wahalar magani.

Sai kuma rashin kyautata wa iyaye da dangi. Yawanci a ƙasar Hausa in dai namiji yana da hali, za a ga yana yi wa iyaye da ‘yanuwa har ma da abokanen arziki hidima mai yawan gaske. To duk lokacin da aka samu akasin haka kuma, wato ba ya wa iyaye da dangi hidima. Ko kuma hidimar da yake musu ba ta kai yadda suke tsammani ko son ya dinga yi musu ba, sai a ɗauki gaba da matarsa. A ce ya tattare a gindinta. Musamman ma idan ana ganinta fes-fes kullum ita da ‘ya’yanta.

Ko da kuwa ita matar tana da wata sana’a da take yi dai ba za ta fita a wajen waɗancan surukai ba. Su kawai duk abinda ta yi ɗansu ne ya yi. Haka kurum sai a ɗauki karan tsana a ɗora wa baiwar Allah.

Zargi da rashin fahimtar juna: Wannan shi ma wata hanya ce da take kawo tangarɗa a alaƙa tsakanin mutane. Zargi mugun abu ne da musulunci ya yi hani da shi. Yanke wa wani hukunci a igiyar zato yana ɓata alaƙa sosai. Shi zargi shi ne mutum ya dinga tunani ko zaton abinda babu shi.

Misali mutum ya yi abu kai kuma ka dinga tunanin wani abu daban da ba shi yake nufi ba. Kuma rashin fahimar halin juna shi yake kawo zargi. Idan surukai ba za su yi amfani da zahiri wajen mu’amalantar juna ba, sai dai a ɗora komai bisa zargi, to lallai za a samu matsalar rashin jituwa.

Misali kamar mace da miji suna zaman lafiya cikin soyayya da lumana sai a dinga zargin cewa ta asirce mijin har ta mallake shi. Wanda wani lokacin ba gaskiya ba ne. Hakan zai sa surikai su ƙullace ta. Musamman ma idan bayan aurenta ɗansu ya daina yi musu hidima yadda ya saba. Ba za a duba hidimomi ne suka ƙaru a kansa ba. Yanzu yana riƙe da gidaje biyu ne a maimakon guda ɗaya kacal da yake riƙewa a da.

Ina fata dai masu karatu za su karanta a nutse su yi mana alƙalanci su ga wai shin wanne ɓangare ne yake da laifi? Iyayen miji ne, ko na mata, ko kuma matar ɗa ko mijin ‘yar? Kuma ina fata waɗanda suke da waɗannan halaye su yi ƙoƙari su gyara.

Domin yau gare ka ne, gobe ga wani. Ma’ana idan ka yi amfani da wata dama ka cutar da wani, gobe kuma Allah zai iya ba wa wani dama kai ma ya cutar da kai.

Sai mun haɗu a wani makon.