
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An bayyana sunayen masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba guda 37 da suka rasu a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Neja a makon da ya gabata.
Mamatan suna daga cikin waɗanda aka kama a wani atisaye da jami’an NSCDC na jihar suka ƙaddamar a ranakun 15 da 16 ga Satumba a yankin Rukunin Gidajen Laftanal Janar Mohammed Inuwa Wushishi da ke Minna, babban birnin Neja.
Dakataccen Kwamandan NSCDC a jihar, Suberu Aniviye a wata sanarwa, ya ce an samu da dama daga cikin waɗanda kama sun rasu a safiyar ranar Alhamis sakamakon “ɓarkewar wata cuta”. Bayan haka ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shi tare da umartar a gudanar da cikakken bincike kan al’amarin.
Hukumar Kare ‘Yan Ɗan-Adam ta Ƙasa-da-ƙasa (IHRC) ta ce tana da cikakken sunayen mutane 37 ɗin da suka rasu. Jakadan zaman lafiya na Ƙasa-da-ƙasa a IHRC, Awaisu Giwa a ranar Lahadi, ya ce sun samu jaddawalin sunayen mamatan daga Babban Asibitin Minna bayan Daraktan Lafiya (CMD) ya bayar da umarnin a ba su rahoton sunayen.
Ya ce, an ƙara wasu sunaye guda huɗu bayan ‘yan uwan wadannan abin ya shafa sun sanar da hukumar cewa babu sunayen makusantansu da suka rasu a lamarin. Giwa ya kuma ce za a yi amfani da sunayen jaddawalin wajen nema wa iyalan mamatan diyya bisa iftila’in da ya shafe su.
Ga cikakken sunayen mamatan:
Ibrahim Sani
Fahad Sa’adu
Abdulsalam Ismail
Usman Aliyu
Abubakar Alhaji
Sani Nasir
Sanusi Khalid
Ahmad Aliyu
Safiyanu Abdullahi
Suleiman Dantala
Idris Haruna
Sani Yakubu
Safiyanu Abubakar
Abdullahi Abubakar
Abubakar Musa
Abdul Mudassir
Suleiman Lawal
Usman Abdullahi
Samuel Sambo
Ibrahim Musa
Yusuf Nasiru
Umar Lawal
Isyaku Amisu
Bissallah Adamu
Abdulbari Suleiman
Shafisu Lado
Usman Ahmad
Usman Ibrahim
Sani Isyaku
Musa Ibrahim
Idris Bashir
Kabiru Suleiman
Emmanuel Emeka
Mu’awiya AbdulKarim — bai cikin jaddawalin Babban Asibitin
Abdul Gafar Abubakar — bai cikin jaddawalin Babban Asibitin
Usman Haruna — bai cikin jaddawalin Babban Asibitin
Yaro Salihu Soba — bai cikin jaddawalin Babban Asibitin.


