
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani mai sana’ar POS da dillalin kayan babur mai suna Isiyaku Nasiru a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina sun shiga hannun hukuma bisa zargin su da hannu a taimaka wa jagoran ‘yan bindiga, Kachalla Muhammadu wajen hada-hadar miliyoyin nairori.
Hukumar Tsaro ta Katsina State Watch Corps ne ta kama Nasiru tare da wasu mutane uku: Abubakar Sayaya, Nura Baka Sati da Ubale Mai Cange. An kama su a wurare mabambanta a jihar a tsakanin ranakun Alhamis da Asabar.
Shugaban ƙaramar hukumar Matazu, Shamsuddeen Muhammad Sayaya, wanda ya tabbatar wa manema labarai kamen, ya ce ana zargin mutanen ne da yin wasu harƙalloli da jagoran ‘yan bindigar.
Ya bayyana cewa, ana gudanar da bincike akansu, inda ake sa ran kamen zai taimaka wa jami’an hukumomin tsaro wajen samun bayanai masu muhimmanci ga ayyukan fallasa tsare-tsaren ‘yan ta’adda da ƙoƙarin daƙile su a yankin. Ana zargin cewa ta hannun Nasiru ne ake ƙulla hada-hadar kuɗaɗen da aka alaƙanta su da Muhammadu waɗanda ake amfani da su wajen siyo makamai da wasu ababen amfanin yau da kullum.
Ƙaramar Hukumar Matazu dai na ɗaya daga cikin yankuna da hare-haren ‘yan bindiga ke shafa a Katsina, ciki har da kashe-kashe, garkuwa, ɗaiɗaicewa da kuma lalata hanyoyin tattalin arziƙi acikin al’umma, lamarin da ya yi sanadiyyar mayar da wani ƙauye da ya shahara da noma a matsayin wajen da jama’a suke fafutukar rayuwa.
A watannin baya ne dai aka yi garkuwa da marigayi Manjo-Janar Rabe Abubakar, tsohon daraktan yaɗa labaran hedikwatar tsaron Nijeriya a yankin Ji-ƙamshi da ke Matazu. An sace shi ne tare da matarsa Amina Abubakar a ranar 30 ga Mayu, 2026 a lokacin da suke kan hanyar tafiya a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton-ɓauna. Daga bisani Manjo-Janar Rabe ya rasu a hannun ‘yan bindigar, amma an ceto matar tasa daga bisani.
