
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago ya yi kira da a samar da doka daga Fadar Shugaban Ƙasa ko Ma’aikatar Ci-gaban Albarkatun Ƙasa ta Tarayya da za ta haramta ayyukan haƙar ma’adinai a yankunan da ake da damuwa akansu a jihar, yayin da a ranar Lahadi Hukumar Sibil Difens (NSCDC) ta gurfanar da dakataccen daraktanta na Neja, Suberu Aniviye da sauran jami’an da suke da alaƙa da mutuwar waɗanda ake zargi da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa doka ba su 37 a ofishin NSCDC.
Bago ya yi wannan kira ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi a lokacin da yake tattaunawa kan iftila’in da ya shafi ‘yan Neja da jami’an NSCDC na jihar yayin da hedikwatarta da ke Sauka a Abuja ita ma ta bayar da ba’asi ga ‘yan jarida kan abin da ta gano game da al’amarin da gurfanar da jami’an da ake bincike akansu.
A cewar Bago, gwamnatin jihar tana buƙatar iko mai ƙarfi daga Gwamnatin Tarayya saboda iyakance yankunan da dokar haƙo ma’adinai za ta riƙa aiki akansu, yana mai cewa lallai akwai buƙatar matakin tarayya domin magance matsalolin yankunan haƙar ma’adinai da yawaitar shigar matasa masu ƙarancin shekaru cikin harkar.
Gwamnan ya bayyana cewa, aikin haƙar ma’adinai ba bisa doka ba ya zama babban ƙalubale ga jihar Neja musamman ganin yadda ƙananan yara suke shiga harkar haƙo ma’adinai ta amfani da salon gargajiya a madadin zuwa makaranta. Bago ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ta samun labarin kamen ne bayan yaɗa batun mutuwar ya karaɗe kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa hakan na da alaƙa da ƙarancin ikon kula da lamuran hukumomin tarayya a jihohi.
Kazalika, gwamnan ya ce “Na ga gawarwaki da dama a ƙasa,” sannan wasu daga cikin su ma ba masu haƙar ma’adinai ba ne, yana mai cewa rukunin gidaje ne wajen ba na haƙo ma’adinai mai lasisi ba.
Kalaman gwamnan na zuwa ne yayin da a ranar Lahadi NSCDC ta gurfanar da Suberu Aniviye da wasu jami’ai da aka alaƙanta su da mace-macen. An gurfanar da su ne a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda rahotanni suka ce jami’ai 24 ne lamarin ya shafa, ciki har da Aniviye da wasu 23.
