Jama’a sun hallaka matashin da ya kashe matar aure da adda a Zamfara

Spread the love

Wani matashi mai suna Hassan ɗan Chanji ya hallaka wata matar aure mai suna Rakiyaya, matar Malam Maikuddi, a ƙauyen Dambo da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara, lamarin da daga bisani ya rikiɗe zuwa ramuwar gayya inda shi ma ya rasa ransa.

Wani mazaunin ƙauyen, Malam Tukur Dambo, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis bayan wata hatsaniya ta ɓarke tsakanin wanda ake zargi da marigayiyar.

A cewarsa, bayan cacar baki ta tsananta, matashin ya shiga cikin gida ya ɗauko adda, inda ya sare matar har ta mutu. Lamarin ya jefa al’umma cikin firgici da alhini, musamman ganin yadda rikici na cikin gida ya rikiɗe zuwa asarar rayuka biyu a lokaci guda.

Majiyar ta ce, bayan da iyalan matar suka tabbatar da rasuwarta, sun bi sawun wanda ake zargin, inda suka kama shi suka yi masa duka har shi ma ya mutu. Wannan mataki ya ƙara dagula yanayi a ƙauyen, yayin da jama’a ke nuna damuwa kan yadda rikici ke yawaita ɗaukar irin wannan mummunan salo.

An rahoto cewa jami’an tsaro sun ɗauki gawawwakin mutanen biyu zuwa Babban Asibitin Bakura domin gudanar da bincike da gwaje-gwaje kamar yadda doka ta tanada. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba, duk da yunƙurin jin ƙarin bayani kan matakan da ake ɗauka dangane da lamarin.

Al’ummar yankin sun bayyana alhini kan faruwar lamarin, suna kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a kan hanyoyin warware saɓani ba tare da tashin hankali ba, domin kauce wa irin wannan mummunan ƙarshe.

By ukarofi