Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar shirya Jarrabawar JAMB ta amince da yin kuskure wajen fitar da sakamakon wasu ɗalibai da suka rubuta jarrabawar ta wannan shekarar ta 2025 (UTME).
A ranar Talata ce hukumar ta sake komawa da baya domin duba sakamakon jarrabawar ɗaliban tare da sauran masu ruwa da tsaki bayan samun ƙorafe-ƙorafe na samun ƙarancin maki da wasu ɗalibai suka yi duk kuwa da ƙwazo da suke da shi.
A yayin da yake magana kan sakamakon sake duba jarrabawar a ranar Larabar nan, rajistaran hukumar, Is-haƙ Oloyede, ya nemi afuwar ɗaliban yana mai amsa cewa sun yi kuskure.
Mista Oloyede ya ce hukumar ta yanke shawarar sake ba wa daliban da wannan abu ya rutsa da su – har 157 daga cibiyoyin rubuta jarrabawar 882 – tabbacin cewa za su sake rubuta jarrabawar daga ranar Juma’a 16 ga watan Mayu.
“Don haka muna roƙon ɗaliban da wannan abu ya shafa su karɓi uzurinmu ba tare da ƙarin gishiri a kai ba. Ina mai ba da haƙuri da ɗaukar alhakin dukkan abin da ya faru,” ya bayyana.
“Mun yanke shawarar ba wa ɗalibai 157 daga cibiyoyin rubuta jarrabawar 882 damar sake rubutawa kuma za mu tuntuɓe su domin su rubuta jarrabawar a ranar Juma’a, 16 ga watan Mayu, 2025.”
A makon da ta gabata ce hukumar JAMB ta fitar da ƙididdigar jarrabawar inda Manhaja ta rawaito muku yadda hukumar ta ce kaso 78% suka samu maki ƙasa da 200.
Wannan lamari ya jawo cece-ku-ce ganin yadda hakan ke baazana ga samun gurbin karatu ga ɗalibai dama a jami’o’in ƙasar musamman waɗanda ke da sha’awar karanta manyan kwasa-kwasai.
Kuma waɗannan ƙorafe-ƙorafe ne suka tilasta wa hukumar kafa kwamiti na musamman da zai sake bibiyar sakamakon wanda kuma shugaban hukumar da kansa ya amsa cewa sun yi kuskure wajen fitar da sakamakon wasu ɗalibai.
Yanzu dai hakan na nufin a ranar Juma’a, 16 ga watan da muke ciki, dalibai sama da 100 za su sake rubuta wata jarrabawar ta JAMB.
