Rayuwar AIG Ammani mai ritaya abar koyi ce ga ’yan sanda – CP. Ahmad 

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Jigawa, CP Ahmad T. Abdullahi ya bayyana cewa, yadda rayuwar AIG Ahmad Ammani Malumfashi mai ritaya a aikin ɗan sanda ta kasance rayuwa ce abar koyi ga kowanne ɗan sanda da ma sauran al’umma a ko’ina suke.

Ya ce, rayuwar AIG Ammani Malumfashi rayuwa ce ta tsoron Allah da ake cewa taƙawa da Amana da kyakyawar mu’amala da sanin ya kamata kuma wannan ce sirrin gama kammala aikin AIG Ammani mai ritaya lami lafiya salin alin kamar dai yadda kwamishinan na jihar Jigawa Alhaji Ahmad T Abdullahi ya bayyanawa manema labarai a lokacin liyafar cin abincin da aka shiryawa tsohon mataimakin ‘yan sanda mai kula da shiyya ta ɗaya Alhaji Ahmad Ammani Malumfashi wanda ya kammala aikin sa da kuma yin ritaya a makon da ya gabata wanda aka shirya masa liyafar cin abinci a Lebanon Club da ke Unguwar Bomfai da ke birnin Kano a ranar Asabar da ta gabata.

Haka kuma ya jaddada mahimmanci koyi da halaye na riƙon addini da Alhaji Ahmad Ammani tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Mai Ritaya don haka babban burin su shi ne yin kyakyawan ƙarshe a wannan aiki da ma wannan duniya baki ɗaya.

Shi ma ɗaya daga cikin dattawan Kano Alhaji Abba Tahir Hungu addua yayi da fatan alheri da wannan mashahurin ɗansanda tsohon mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya AIG Ahmad Ammani Mai Ritaya wanda Alhaji Abba tahir ya buƙaci ɗaukacin matasan ‘yan sanda da sauran maaikata da ɗaukacin alumma a duk inda mutum ya samu kansa ya zauna da mutane lafiya domin shi ne babban arzikin duniya ya kuma shawarci shugabani a ko wanne matakin kan kwatanta adalci da tsoron Allah inda kuma yayi adduar zaman lafiya a Kano da nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

AIG Ahmad Ammani Mai Ritaya ya samu rakiyar yan uwa , ya ya , masoya, abokan aiki, ‘yan kasuwa wajen wannan liyafa ta cin abinci da aka yimasa daga cikin yan uwa akwai Hajiya Rukayya Ammani Malumfashi wacce yaya ga AIG Malumfashi Mai Ritaya sai kuma Hajiya Hauwa Ahmad Ammani Malumfashi wanda a ƙarshe AIG Malumfashi mai ritaya ya shawarci jamian yan sanda da ke faggen aiki kan su haɗa kai da alumma wajen warware matsaloli da suka taso ta cikin alumma wanda hakan zai sa a samu kyakyawan cigaba a wannan aiki da kuma zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin alumma inda ya ƙarƙare da cewa Allah ne ya ƙaddara zaiyi aikin ‘yan sanda domin shi malamin makaranta ne Allah kuma ya ƙaddara haka don haka yana godewa Ubangiji da ɗaukacin al’umma da suka bashi gudunmawa ta addua da sauran goyan baya a wannan aiki da kuma wannan walima ta cin abinci da sauransu.

By ukarofi