Jam’iyyar ADC ta bai wa Kwankwaso kaso 60 na shugabancin jam’iyyar a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ƙungiyarsa ta amince da karɓar ƙaramin kaso na muƙamai a cikin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), duk da cewa an ba su damar samun kaso mafi girma.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a Kano, Kwankwaso ya ce ‘yan tsohuwar jam’iyyar NNPP da suka koma ADC an fara ba su tayin kashi 80 cikin 100 na tsarin jam’iyyar. Sai dai sun zaɓi tsarin rabo na 60–40 maimakon haka.

A cewarsa, wannan mataki an ɗauke shi ne da gangan domin buɗe ƙofa ga haɗin kai da kuma bai wa sauran masu ruwa da tsaki damar shiga cikin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa amincewa da ƙaramin rabo wata dabara ce ta siyasa domin jawo ƙarin jama’a da ƙarfafa haɗin kai, maimakon rinjayar tsarin jam’iyyar gaba ɗaya.

Kwankwaso ya kuma tuna da irin wannan tsarin rabon mukamai da aka yi amfani da shi a baya lokacin da ƙungiyarsa ta sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Dangane da halin da ake ciki a Jihar Kano, tsohon gwamnan ya ce mambobin Kwankwasiyya suna riƙe da manyan mukamai a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, ciki har da shugabancin ƙananan hukumomi. Sai dai ya amince cewa daga baya an miƙa wasu daga cikin waɗannan mukamai bayan koke-koke daga sauran ‘yan jam’iyya.

Ya ƙara da cewa kusan mukamai 10 na ƙananan hukumomi an bar su ne domin daidaita al’amura da kuma tabbatar da adalci a cikin jam’iyyar.

Kwankwaso ya shawarci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa matsa lamba wajen neman mukamai, yana mai jaddada muhimmancin haƙuri da adalci wajen rarraba mukamai.

Haka kuma ya gargadi mambobi da kada su nace wajen ɗora wasu mutane a mukamai, musamman idan ba su cancanta ba, yana mai cewa ya kamata a fifita muradun jam’iyya gaba ɗaya fiye da muradin kai.

By ukarofi