Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ke addabar Nijeriya za a iya kawo ƙarshenta cikin watanni shida kacal idan gwamnatin tarayya ta nuna cikakken ƙuduri.
Ndume ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels Teleɓision, inda ya nuna damuwa kan yadda tashe-tashen hankula ke ƙaruwa, musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Sanatan ya jaddada cewa abin da ake buƙata ba wai yawan koke-koke ba ne, illa ɗaukar matakan da suka dace tare da nuna ƙuduri a aikace.
“Ba batun yin korafi ba ne. Ba batun tambayar mutum kamar ni a matsayina na sanata dalilin faruwar waɗannan abubuwa ba ne. Ni a kullum ina ganin cewa idan Shugaban ƙasa da gwamnatin tarayya sun yi da gaske kan wannan lamari, za mu iya kawo ƙarshen matsalar cikin watanni shida.
“Abin da muke buƙata shi ne mu horar da sojojinmu, mu ba su kayan aiki, mu basu makamai yadda ya kamata, sannan mu ƙarfafa musu gwiwa,” inji Ndume.
Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ake ci gaba da rasa rayukan jami’an tsaro, ciki har da manyan hafsoshi, yana mai cewa hakan na nuna akwai matsaloli a tsarin gudanar da yaƙi da ta’addanci.
“Bayan kashe kwamandojin su, sai su dawo su kashe namu kwamandojin, har yanzu kuma ana rasa jami’ai da dama. Har yau ma, a yankin Arewacin Borno, mun rasa wani kolonel tare da wasu sojoji. Wannan bai kamata ya ci gaba ba. Wannan shi ne babban abin damuwa,” in ji shi.
Ndume ya kuma danganta ƙaruwar rashin tsaro da rashin cikakken aiwatar da tsare-tsaren tsaro yadda ya kamata.
“Yanayin tsaro da ke ƙara tabarbarewa yana da alaƙa da matakan da ake ɗauka amma ba a kammala su yadda ya kamata ba. Dole ne mu yi da gaske kan wannan lamari; dole ne mu aikata abin da muke faɗa,” ya ƙara da cewa.
Dangane da batun taimakon ƙasashen waje, Ndume ya jaddada cewa abin da Nijeriya ke buƙata shi ne ingantaccen bayanan sirri, fasaha da ƙwararrun ma’aikata, maimakon dogaro da sojojin ƙasashen waje.
“Abin da muke buƙata shi ne bayanan sirri. Muna buƙatar tallafin jiragen sama. Haka kuma muna buƙatar ƙwarewar masana. Muna da wasu da aka horar a ƙasashen waje, sojojin musamman. Muna da ƙwararru a cikin ƙasa; abin da suke buƙata kawai shi ne kayan aiki, alburusai da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
“Ba mu da isassun jiragen leƙen asiri (drones). Ku duba abin da Burkina Faso ke yi, fasaha ce. Za mu iya amfani da fasaha wajen kawo ƙarshen wannan matsala ko rage ta cikin gajeren lokaci. Idan aka yi amfani da drones tare da horar da ma’aikata da kafa cibiyoyin kula da su yadda ya kamata, za mu samu nasara,” in ji shi.
Sanatan ya kuma lura cewa Jihar Borno za ta fuskanci matsala mafi muni da ba don ƙoƙarin da Gwamna Babagana Zulum ke yi ba wajen daidaita al’amura a wasu sassan jihar.
Ya yabawa gwamnan bisa matakan da yake ɗauka, yana mai cewa sun taimaka matuƙa wajen rage tasirin matsalar tsaro a jihar.
