Daga JOHN D WADA a Lafia
Jam’iyyar Labour Party (LP) a jihar Nasarawa ta fitar da sakamakon zaɓen fidda gwaninta na ‘yan takaran kujerar gwamna da sanata da majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar.
Shugaban kwamitin zaɓen a jihar Dr. Kalu Ekeh ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Lafia babban birnin jihar inda ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana da gaskiya.
Ya sanar cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Karu/Keffi/Kokona wato Hon. Jonathan Gaza ya fito takar gwamnan jihar a ƙarƙashin LP ɗin inda aka kuma tabbatar da shi ba tare da hamayya ba bisa dokar jam’iyya da dokar zaɓe ta 2026. Kwamitin zaɓen ya kuma ce za a ba shi takardar nasara a ofishin jam’iyya na ƙasa a Abuja cikin mako mai zuwa.
Bayan an tabbatar da shi, Gaza ya yaba wa shugabannin jam’iyya da mambobi bisa amincewa da shi. Ya yi alƙawarin bai wa jihar ta Nasarawa shugabanci mai inganci da haɗin kai da cigaba.
Haka shima tsohon ministan yaɗa bayanai da al’adu Labaran Maku an tabbatar da shi a matsayin ɗan takar sanatan Nasarawa ta Arewa. Za a ga Maku a zaɓen cike gurbi na ranar 20 ga Yuni 2026 bayan rasuwar sanata Godiya Akwashiki sannan kuma a zaɓen 2027.
Wani maisuna Dr. Benjamin Kigbu ne ya wakilci Maku a wajen zaman inda ya ce nasarar ba kawai daraja ga Maku ba ce illa amincewar jama’a da hangen nesa ne.
Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa sauran ‘yan takaran jam’iyyar ta Labour party a jihar da aka tabbatar sun haɗa da
Dr. Emmanuel Akolo-Karu/Keffi/Kokona
Hon. Blanzou Adamu-Akwanga/Nasarawa Eggon/Wamba. Hon. Jesse James Ayenajeh-Lafia/Obi. Hon. Akaba Joshua-Lafia/Obi
Har ila yau jam’iyyar ta LP ta tantance ‘yan takara 13 domin majalisar dokokin jihar ciki har da Asilika Essla da Mohammed Ibrahim da Ashy David Maiyaki da Alexander Abashi Dauda.
Kwamitin zaɓen a karshe ya ƙara da cewa ya gudanar da komai bisa doka kuma hukumar shirya zaɓuka ta ƙasa ta INEC ta kuma sa ido kan zaben cike gurbi na sanatan Nasarawa ta Arewar da sauran duka zaɓukan.
