Jam’iyyar SDP ta zargi Gwamna Inuwa kan cin zarafin shugaban ta a jirgin sama

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Jam’iyyar adawa ta Social Democratic Party (SDP) a Jihar Gombe ta mayar da martani mai zafi kan wata sanarwa da Ismaila Uba Misilli, daraktan yaɗa labarai na Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar, dangane da wani rikici da ya faru tsakanin Gwamnan da muƙaddashin shugaban jam’iyyar SDP, Kwamared Adamu Abubakar Modibbo, a cikin jirgin Sama daga Gombe zuwa Abuja.

A cewar wata sanarwa da Kwamared Modibbo tare da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Injiniya Muhammad Abdulkadir Kumo, suka fitar, SDP ta zargi Gwamna Inuwa Yahaya da nuna halin rashin dattaku da neman tada hankali a lokacin da suke cikin jirgin.

Bisa ga sanarwar, Kwamared Modibbo ya nuna ladabi da girmamawa ga gwamnan a matsayin alama ta kamalar siyasa amma gwamnan ya mayar da martani cikin faɗa har da yunƙurin amfani da ƙarfi.

Sanarwar ta ƙara bayyana cewa, duk da wannan yanayi, Kwamared Modibbo ya ci gaba da nuna haƙuri ba tare da mayar da martani mai tsanani ba, koda yake rikicin ya tsawaita har zuwa lokacin da jirgin ya sauka a Abuja.

Jam’iyyar SDP ta yi watsi da sanarwar da tawagar gwamnan ta fitar, tana mai cewa hakan wani ƙoƙari ne na ɓoye gaskiya. SDP ta zargi gwamnatin Gombe da yin ƙaryar da ke da nasaba da “ɓata suna da ɓoye gaskiya.

“Muna ƙalubalantar tawagar gwamnan da ta fitar da hujjoji domin ƙaryata faruwar lamarin maimakon dogaro da abin da ta kira “maganganun marasa ma’ana.”

“Wannan yunƙurin ɓoye gaskiya ya nuna yadda wannan gwamnati ke da rashin kyakkyawar ɗabi’a, rashin kula da haɗin kai, da rashin mutunta muryoyin ‘yan adawa,” inji sanarwar.

SDP ta sake jaddada ƙudurinta na samar da ingantacciyar shugabanci ga al’ummar Jihar Gombe, tana mai cewa tsoratarwa da halayen rashin juriya ba za su sa ta sauya matsayarta ba.

Jam’iyyar ta yi kira ga jama’a da su yi la’akari da halayen shugabanninsu tare da nuna buƙatar ladabi, da girmama ƙa’idojin dimokuraɗiyya a jagoranci.

Wannan rikici ya sake bayyana irin tashin hankalin da ke ƙaruwa tsakanin jam’iyya mai mulki da jam’iyyar adawa a Jihar Gombe, lamarin da ke haifar da damuwa kan zaman lafiya da mutunta juna a siyasar jihar.

By ukarofi