Sojoji sun kashe gomman ƴan bindiga da tarwatsa maɓoyarsu a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun haɗaka na Atisayen ‘FANSAN YAMMA’ a Zamfara, sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga da dama a maɓoyarsu dake gabashin Ƙaramar Hukumar Ƙauran-Namoda a jihar.

A ranar 10 ga watan Maris ne jami’an suka kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar ƴan ta’addar da ƙwato makamai da wasu ababe.

Dakarun, waɗanda ke aiki a ƙarƙarshin Birget ta 1, sun kai farmakin ne ta sama da ta ƙasa a maɓoyar babban ɗan ta’adda, Ɗan Sa’adia.

Daga cikin waɗanda aka kashe a yayin farmakin akwai shahararren ɗan bindiga mai suna Babangida.

Harin dakarun ya sa an ƙwato ƙaramar bindiga ta gida ƙirar pistol, da wata bindigar gargajiya da kuma mazubin harsasai a maɓoyar.

Haka kuma, sojojin sun tarwatsa wata maɓoyar ƴan ta’adda a yankin Gidan Rugga inda suka ƙwato inifom ɗin sojoji guda biyu da takalmin sojoji na mutum biyu da kuma wasu cazozin rediyo.

Bugu da ƙari, dakarun sun buɗe hanyar Kungurƙi-Walo, wadda ƴan ta’addar suka addabi masu amfani da ita wajen shiga ko fita zuwa wasu ƙauyuka da hakan ya sa aka rufe ta a baya.

Babban jami’in yaɗa labaran dakarun ‘FANSAN YAMMA’, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana cewa, jami’an suna ƙoƙari wajen daƙile ayyukan ƴan bindigar da tarwatsa mafakarsu don dawo da gudanar harkokin tattalin arziƙi da zaman lafiya mai ɗorewa a shiyyar.

Ya yi kira ga mazauna yankunan da su cigaba da ba su haɗin kai don tabbatar da dawo da tsaro a yankin da ma jihar baki ɗaya.

By Babaji