Majalisar Dokokin Katsina ta amince da Naira biliyan 245.4 a matsayin kasafin kuɗi na ƙananan hukumomi 34

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin ƙananan hukumomi da masarautar, Hon Ibrahim Ɗanjuma Machika ya bayyana haka yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin a zauren majalisar.

Makon da ya gabata, kwamitin ya gayyaci shugabannin ƙananan hukumomi inda suka kare kasafin kuɗi na shekarar 2025.

Kwamitin ya bada shawarar duba yiwuwar samar da ofis na musamman da zai kula da kasafin kuɗi a kowace ƙaramar hukuma.

Haka kuma kwamitin ya buƙaci ma’aikatar ƙananan hukumomi da masarautu da ta shirya bada horo lokaci lokaci ga shugabannin ƙananan hukumomi.

Sauran shawarwari sun haɗa da kira ga ƙananan hukumomi da ƙara himma wajen tara kuɗin shiga.

Daga ƙarshe majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin ta,Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya amince da ƙudirin dokar,inda ya umarci akawun majalisar ya miƙa ga ɓangaren zartarwa.

By ukarofi