Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta amince da naɗin CP Dakta Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon Kwamishinan yan sanda na Jihar Kano.
Bakori, wanda ya fito daga Jihar Katsina, ya maye gurbin CP Salman Garba Dogo, wanda aka ɗaukaka zuwa matsayi na mataimakin sufeto ƴan sanda (AIG).
Kafin naɗinsa, CP Bakori ya yi aiki a matsayin Kwamishinan ƴan sanda na Homicide a ofishin binciken laifuka na ƴan Sanda (FID) da ke Abuja.
Sannan ya samu muhimman muƙamai da dama a cikin rundunar ‘yan sanda, ciki har da Kwamanda na rundunar haɗin gwiwar Bayelsa (Operation Doo Akpo), Yenagoa; Mataimakin kwamishina a sashin kariya na musamman (SPU), hedkwatar rundunar ƴan sanda, Abuja da mataimakin kwamishina a sashin binciken laifuka (CID), Jihar Bayelsa.
Sauran muƙaman da ya riƙe sun haɗa da mataimakin kwamishina a CID na Jihar Ribas; babban jami’I na Kwamishinan ƴan sanda da kwamanda na 17 PM, Akure.
Shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, DIG Hashimu Argungu (rtd), ya ƙalubalanci Bakori kan ya tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.
“Dole ne ka saurin shiga cikin wannan aikin mai cike da ƙalubale da ke gabanka, ka tabbatar da cewa an kawo ƙarshen laifuka da aikata laifi, tare da inganta ƴancin zirga-zirga da tsaron harkokin kasuwanci,” in ji Argungu.
Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan ci gaban sa da kuma bayar da goyon bayan da ake buƙata domin samun nasara.
