Jam’iyyu 18 ke fafutikar neman kujerar gwamnan Anambra – INEC

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa 18 ne su ka nuna sha’awar su ta shiga zaɓen gwamnan Jihar Anambara da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba mai zuwa.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron kwata ta biyu na hukumar da jam’iyyun siyasa wanda aka yi a ranar Alhamis a Abuja.

Yakubu ya ce dukkan jam’iyyun 18 sun tsara gudanar da zaɓuɓɓukan su na fidda gwani a bisa jadawalin kwanaki da hukumar ta fitar.

Ya ce, “A kan batun zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin Yankin Birnin Tarayya, jam’iyyun siyasa sun gama zaɓuɓɓukan su na share fage a mazaɓu 68 da su ka haɗu su ka yi shugabannin ƙananan hukumomin guda shida da kansiloli 62.

“Jimillar jam’iyyu 14 daga cikin 18 sun zaɓi ‘yan takara 110 na muƙaman Shugaba da Mataimakin Shugaba da kuma ‘yan takarar zama kansila su 362.

“Gaba ɗaya dai, jam’iyyu 14 sun fitar da ‘yan takara 472 da za su nemi kujeru 68 a Yankin Babban Birnin Tarayya.

“Akwai zanen taswira da aka yi mai nuna rabe-raben ƙananan hukumomin a cikin wannan jakar kwalin ta wannan taron da mu ka ba ku.”

Yakubu ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun da su riƙa yin kira ga ‘yan takarar su a zaɓen gwamnan da na ƙananan hukumomin da ke Yankin Birnin Tarayya da sauran zaɓuɓɓukan cike gurbin da ke tafe da su tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce, “Kamar yadda ku ka sani, akwai zaɓuɓɓukan cike gurbi da na ƙarshen wa’adi da aka shirya gudanarwa kafin Babban Zaɓen 2023.

“A ƙarshen wannan makon, za a yi zaɓuɓɓukan cike gurbi guda biyu a Jihar Kaduna, wato na Mazaɓar Jiha ta Sabon Gari inda jam’iyyu biyar su ka bayar da ‘yan takara, da Jihar Jigawa na Mazaɓar Tarayya ta Gwaram wanda jam’iyyu goma su ka shiga.

“Mun kammala dukkan shirye-shirye na waɗannan zaɓuɓɓukan cike gurbin, wanda ya haɗa da tabbatar da isar muhimman kayan aiki a yau zuwa mazaɓun biyu. Zuwa yanzu dai, babu wata hatsaniya a cikin shirye-shiryen.

“Mu na kira a gare ku da ku ja hankalin ‘yan takara da magoya bayan ku da su ci gaba da tabbatar da zaman lumanar da ke akwai yanzu.

“A game da sauran zaɓuɓɓukan share fage da su ka rage, ina tabbatar maku da cewar da zaran an samu guraben da Kakakin Majalisar Wakilai ya bayyana, za mu fitar da jadawalin lokacin yin su, wato jadawalin lokacin zaɓen Mazaɓar Tarayya ta Jos ta Arewa/Bassa da ke Jihar Filato da na Mazaɓar Tarayya ta Lere da ke Jihar Kaduna.”