Jarrabawar rayuwa ce ta sa na zama uwar marayu – Maryam Nabage

“Aikin jin ƙai ko tallafa wa mabuƙata ba ruwansa da addini”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Sunan Hajiya Maryam Shehu Nabage da ake yi wa laƙabi da Uwar Marayu, ba ɓoyayye ba ne a cikin garin Jos da ma Jihar Filato bakiɗaya, saboda yadda ta yi fice wajen tallafa wa marayu, gajiyayyu, zawarawa da almajirai ƙarƙashin gidauniyarta ta Haske Support Foundation. Wakilin Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya ziyarci gidan ta dake Tudun Osi a unguwar Nasarawa Gwong, inda ya tarar da ita cikin tsakiyar aikin rabon kayan azumi da na ɗinkin sallah ga yara marayu. Ga yadda hirar su ta kasance:

MANHAJA: Hajiya, ko za ki gabatar mana da kan ki?
MARYAM NABAGE: Alhamdulillahi. Sunana Maryam Shehu Nabage. Haifaffiyar garin Jos ce ni, kuma a nan na yi rayuwa ta har na girma, na yi aure. Ina da iyali, yarana shida. Kuma ina kasuwanci da harkar ba da maganin gargajiya. Na sadaukar da rayuwata da duk abin da na mallaka wajen aikin taimakon al’umma, musamman ga marayu da marasa ƙarfi. Na riƙe wasu yaran marayu da suka girma a hannuna, na sanya su a makaranta, har na yi mu su aure, a ciki ma har da mai aikin jinya. 

Yaya batun karatu fa?
Na yi karatun addini, na samu karatun Alƙur’ani da littattafan fiƙihu, amma ban yi karatun boko mai zurfi ba. Shi ya sa na dage wajen bai wa yarana da sauran marayun da na riƙe ilimi mai inganci, wanda za su taimaki rayuwar su da ta sauran al’umma. Alhamdulillahi, kawo yanzu dukka yarana suna da digiri, wasu ma suna kan cigaba da karatu.

Me ya ja hankalinki kika fara wannan aiki na ba da tallafi ga marayu da sauran mabuƙata?
A gaskiya na taso da rashin gata, ban zauna a gaban iyayena na samu kyakkyawar kulawar da ta kamata yaro ya samu ba. Kuma wannan na daga cikin dalilan da suka sa ban samu na yi karatun boko kamar sauran yara ba. Shi ya sa a duk lokacin da na ga wani mutum cikin halin ƙunci da rashin abinci, rashin lafiya ko rashin karatu, sai in ji duk hankalina ya tashi, saboda ina tuna lokacin da nima nake cikin irin wannan halin. Na kasance ni mace ce mai yawan tausayi, ba na son in ga mata da qananan yara suna cikin damuwa na rashin yadda za su yi da ƙuncin rayuwar da suke ciki. Tun da na ga na fara samun rufin asiri, sai na ga bai kamata in riƙe ni kaɗai da iyalina ba, don haka na shiga wannan hidima ta taimakon jama’a fiye da shekaru 30 kenan. Daga bisani har na kafa Gidauniyar Haske Support Foundation, da taimakon yaran da suke tallafa min, muna shiga unguwanni, ƙauyuka, har ma da wasu makwaftan jihohi kamar Jihar Bauchi, Jihar Kano da Jihar Kaduna. Muna taimaka wa marayu, nakasassu, almajirai, matan da suka rasa mazajen su na aure ko suke rayuwa cikin ƙuncin rayuwa da sauran su, ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ba.

To, Hajiya wacce harka kike yi da kike samun kuɗaɗen da kike waɗannan ayyukan alheri haka?
Ai kamar yadda na gaya maka a farko, ni ‘yar kasuwa ce. Amma na fara ne da harkar ba da maganin gargajiya, ina taimaka wa marasa lafiya tsawon shekaru 30 kenan, daga baya na ga ya dace in samu wata harka ta kasuwanci da zan riƙa juya ɗan abin da nake samu ina wasu ayyukan alheri da su. Wannan ne ya sa na shiga harkar saye da sayarwa, ina sayen ƙadarori kamar gidaje da filaye ina sayarwa. Ina kuma saya wa manoma takin zamani idan lokacin noma ya yi, bayan girbi sai su biya ni da hatsi. Wani lokaci kuma ina sayen kayan abinci da kuɗina ina tarawa, don taimaka wa jama’a. Ina ba da ɗanyen abinci kuma ina dafa wa ana raba wa almajirai da masu buƙata safe da yamma, kullum.

Bayan da na fara waɗannan ayyuka na taimaka wa mabuƙata kuma na riqa samun tallafi daga wasu masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da suke yaba wa da abubuwan da suka ga ina yi, saboda amince wa da yarda. Wasu ma ba ƙungiyoyin Musulmi ba ne. Wani lokaci sukan ba ni kuɗi, ko kayan abinci ko sutura da za a raba wa gajiyayyu da marayu. Kamar irin su Alhaji Ibrahim Musa Uja, Hajiya Mairo Musa da ke Abuja. Alhaji Abdullahi Maisango Gamel, wanda ya kai shekara 10 yana kawo min kayan abinci, idan watan azumi ya kama, don raba wa ga muskinai. Akwai wata mata ma da ta tava bani gudunmawar Naira ɗari biyar, na sayi gishiri ana sa wa a girkin da ake yi ana rabawa almajirai, saboda ita ma lada take nema.

An ce ayyukan naki sun ma ƙetare Jihar Filato har da wasu jihohi, wanne taimako kike ba su?
Eh, haka ne. Na gina Masallacin Jumma’a a garin Falali da ke ƙaramar hukumar Takai a Jihar Kano, na kuma gina wani a Ƙaramar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa, sannan akwai kekunan guragu da na tallafa wa gwamnatin Jihar Kano da su. Haka ma a Jihar Kaduna, ta yankin Saminaka nan ma na ba da tallafi da dama. Yanzu haka a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi na sayi wani babban fili da nake so na gina asibiti, don taimaka wa al’ummar ƙauyukan da ke kewayen wajen musamman mata masu juna biyu, sakamakon wani abin tausayi da na gani, wani lokaci na shiga yankin don harkar gawayi da nake saye ina sayarwa, sai na ga an fito da wata bafulatana daga wani lungu ana neman yadda za a kai ta asibiti, amma saboda rashin asibiti a kusa haka ta rasu kafin ma a fito bakin hanya.

Wannan abin tausayi da na gani ya sa na ga lallai ya kamata na yi wani abu, don tallafa wa mutanen yankin. Shi ya sa na sayi wannan filin da yanzu haka na ke shirin fara aikin ginin asibitin, har ma Mai Martaba Sarkin Bauchi da ya ji labarin ƙoƙarin da nake son yi, ya yi alƙawarin tallafa wa shi ma don aikin ya samu nasara.

Wanne ƙoƙari gidauniyarki ta Haske Support Foundation take yi a ɓangaren inganta tsaro da zaman lafiya, don na ji kina cewa har waɗanda ba Musulmi ba ma kuna hulɗa da su?
Babu shakka muna aiki kafaɗa da kafaxa da ƙungiyoyin taimakon al’umma irin na ‘yan banga masu aikin sa kai don magance matsalolin tsaro, muna taimaka musu da kayan aiki ko kuɗin sa mai a motocin aikin sintiri, ba su kaɗai ba, har ma da jami’an ‘yan sanda. Sannan a ɓangaren zaman lafiya, na ziyarci Ƙaramar Hukumar Riyom, inda ake yawan samun rikicin ƙabilanci tsakanin Fulani makiyaya da manoma ‘yan ƙabilar Birom, don ƙarfafa musu gwiwar zaman lafiya da juna. Kuma duk shekara akwai kayan Kirsimeti da ake raba wa yaran Kirista, da takalma, ko kayan abinci da muke bayarwa unguwa unguwa, ba a cikin Jos kaɗai ba, har ma da wasu ƙananan hukumomi, kamar Jos ta Kudu, Jos ta Gabas, Mangu da Riyom. Don aikin jin ƙai ko tallafa wa mabuƙata ba ruwan sa da addini hatta dabba ana son a taimaka mata. Don malamai sun koyar da mu cewa, akwai matar da ta taimaka wa kare ya sha ruwa daga takalmin ta, a dalilin haka ta samu gafarar ubangiji, duk da kasancewar ta karuwa. 

Yanzu ga shi na same ki kina ta fama da raba wa yara atamfofi da shaddoji don su yi ɗinkin Sallah. Anya abubuwan ba su miki yawa ba kuwa? 
Ai aikin alheri ba ya yawa, kuma ba ya kaɗan, matuqar za a yi shi da kyakkyawar niyya. Mutum bai san aikin da zai yi Allah ya karɓa ya yi masa rahama da gidan Aljanna ba. Na fi shekara 10 ina wannan taimakon na kayan Sallah, ina raba wa yara ne marayu da marasa gata da nakasassu, waɗanda ba su da mai yi musu ɗinkin sallah. A wannan shekarar kaɗai mun raba wa yara fiye da ɗari 5 kayan Sallah, tsakanin unguwanni da ƙungiyoyi waɗanda muka bi ta hannun su don isa ga wasu marayu da ke ƙarƙashin kulawarsu. 

Wanne yabo da ƙarfafa gwiwa kike samu daga ɓangaren jama’a da gwamnati ko ƙungiyoyin da kuke hulɗa da su?
E, to. Kamar dai yadda a baya na faɗa, akwai mutane masu hali da ƙungiyoyi da suke tallafawa, amma a ɓangaren gwamnati kam babu. Hana rantsuwa dai lokacin zaman kulle na yaqi da yaɗuwar annobar Korona, shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman ya ba mu tallafin taliya katan 40. Sauran ayyukan da nake yi daga asusuna ne da ɗan abin da nake sannu na ribar kasuwanci da nake yi. Sai kuma shaidar karramawa da nake samu daga ƙungiyoyi na ciki da wajen Jihar Filato da suke ƙarfafa min gwiwa kan ayyukan da nake yi, har ma da rundunar ‘yan sanda.

Akwai wani taimako ko tallafi da kike buqata don ci gaba da ayyukan da kika saba yi?
A gaskiya babu abin da zan ce wa Allah da sauran al’umma masu taimakawa, sai godiya. Sai dai ina roƙon waɗanda Allah ya hore wa su ci gaba da taimaka mana, musamman da kayan abinci, saboda yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa wasu samun ɗanyen abinci kamar hatsi ko shinkafa yana taimakawa sosai. Don za ka ga magidanci ya zo neman abinci saboda ya fita bai samu ba kuma gida babu wanda za a dafa a ci. Sai kuma kuɗi don tallafawa marasa lafiya a asibitoci da makarantun yara marayu da nake ɗaukar nauyin karatun su. Ina samun masu neman taimakon kuɗin magani ko na sallama a asibiti, saboda ba su da yadda za su yi. Idan aka samu kuɗi da kayan abinci ba ƙaramin taimakawa za su yi ba.

A ƙarshe, wanne kuka ko roƙo kike da shi ga gwamnatin Jihar Filato ko wasu hukumomin da abin ya shafa?
Masha Allah. A gaskiya ni roqona ɗaya ga gwamnatin Jihar Filato, shi ne, a ƙarasa gyara mana titin da ya bi ta gaban gidana a nan Tudun Osi, wanda aka fara tun 2014 lokacin tsohon Gwamna Jonah Jang, amma an yi watsi da aikin. Ga shi an kankare hanyar an baza jar ƙasa, an datse hanyar da muke samun ruwan famfo, tsawon waɗannan shekaru an kasa gyarawa. Sai rayuwa muke yi cikin ƙura da jar ƙasa, a dalilin hakan har na gamu da ciwon ƙirji da nake ta faman jinya, yaran gidana marayu su biyu Ishaq da Abubakar sun rasu saboda rashin lafiya mai nasaba da wannan mugunyar ƙura. Na kai kukan ofishin shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, har yanzu abin ya gagara, na rasa inda zan sa kaina kan wannan matsala. Kullum da wannan abin baqin ciki nake kwana a raina. Don Allah gwamnati ta taimaka min da sauran makwafta da muke rayuwa cikin wannan baqin ciki.

To Hajiya, mu na godiya da samun lokacinki.
Ni ma na gode ƙwarai. Allah ya ƙara ɗaukaka jaridun Manhaja da Blueprint.