Jarumin barkwanci Mista Macaroni da VDM, sun magantu kan lamarin ‘yar bautar ƙasa da ake wa barazana

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Shahararren ɗan wasan barkwanci Mista Macaroni, da kuma VDM, wato veryDarkMan da wasu fitattu sun magantu kan lamarin ‘yar bautar ƙasa da ke tada ƙura a kafafen sadarwa a ‘yan kwanakin nan, kan barazanar da ma’aikata ke yi mata bisa sukar gwamnati da ta yi.

Taƙaddar wadda ya samo asali da wani faifan bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna ‘yar bautar ƙasar da ke bayyana irin matsalolin da ke tattare da wannan gamnatin.

Jim kadan bayan haka ne rahotanni suka bayyana cewa, jami’an hukumar NYSC sun gayyaci wannan baiwar Allah, inda hukumar ta yi mata jan ido tare da yi ma ta barazanar ɗaukar matakin ladabtarwa saboda kalaman nata.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Mista Macaroni ya yi tir da wannan lamari, wanda ya kira wani nau’i na zalunci, yana mai jaddada cewa, ‘yan Najeriya na da ‘yancin faɗar albarkacin bakinsu.

“Masu bautar ƙasa, suna yiwa ƙasarsu hidima ne, ba bayin wata gwamnati ba ne! Bai kamata mu malumce wa duk wani tsari da zai hana ‘yan ƙasa faɗar gaskiya ba.”

Hakazalika, veryDarkMan (VDM), wanda ya shahara a fafutukar kare haƙƙi, ya yi kira ga shugabannin NYSC, inda ya buƙace su mutuntata haƙƙin ‘yan ƙasa.

“Idan har ma’aikaci ba zai iya bayyana ra’ayinsa game da gwamnati ba, to wacce irin dimokuraɗiyya muke yi?”

Lamarin dai ya janyo cece-kuce a kan ‘yancin faɗin albarkacin baki, da ƙarfin iko irin na gwamnati, da kuma haƙƙin ‘yan yi wa ƙasa hidima na NYSC a Najeriya.

By ukarofi