
Yayin da al’umma ke ta cecekuce akan hare-haren da ake kai wa Kiristoci, akwai wani ɓangare na gaskiya da aka yi shiru a kai, wato hare-haren da ake kai wa Musulmai a masallatai da suka yi sanadin salwantar ɗaruruwan rayuka a lokacin da suke cikin ibada.
Duk da cewa kalaman tsohon shugaban Amurka Donald Trump na barazanar ɗaukar matakin soja akan Najeriya saboda zargin “kisan gilla ga Kiristoci” sun jawo cece-kuce, PRNigeria ta bankaɗo wani ɓangare mai girman gaske na wannan rikici da duniya ta kasa kula da shi: hare-haren da ake kai wa Musulmai a masallatai da wajen ibada.
Daga 2009 zuwa 2025, dubban Musulmai a yankin Arewa musamman a jihohin Borno, Yobe, Kano, Katsina, Zamfara, da Adamawa, sun gamu da ajalinsu yayin da suke cikin ibada.
Waɗannan hare-hare da Boko Haram, ISWAP, da ƴan bindiga suka kai, sun yi ɓarna mai girma, amma ba su samu irin kulawar da duniya ke bai wa irin wanda Kiristoci ke fuskanta ba.
Ga jerin wasu manyan hare-haren da suka girgiza ƙasa, kamar yadda jaridar ta ruwaito:
11 ga Agusta, 2013 – Konduga, Borno: Boko Haram ta kashe mutane 44–46 yayin sallar Asuba a Masallacin Juma’a.
28 ga Nuwamba, 2014 – Kano: Ƙungiyar ta kai hari a babban masallacin Kano, inda aka kashe fiye da mutum 80.
17 ga Yuli, 2015 – Damaturu, Yobe: Bom ya tashi yayin sallar Idi, ya hallaka kusan mutum 50.
16 ga Maris, 2016 – Molai, Borno: ƴan mata masu bom sun kashe mutum 24 a lokacin sallar Asuba.
21 ga Nuwamba, 2017 – Mubi, Adamawa: Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 50 a cikin masallaci.
25 ga Oktoba, 2021 – Mazakuka, Jihar Neja: Ƴan bindiga sun kashe limami da mutum 18 yayin sallar Asuba.
5 ga Nuwamba, 2023 – Funtua, Katsina: Ƴan bindiga sun kai hari wajen bikin Maulidi, suka kashe mutum 20.
19 ga Agusta, 2025 – Unguwan Mantau, Katsina: Ƴan bindiga sun kashe mutum 27 yayin sallar Asuba.
Wannan jerin ba cikakke ba ne, amma yana nuna yadda Musulmai ke fuskantar hari kai-tsaye a wuraren ibada tun tsawon shekaru fiye da goma.
Yayin da duniya ke ta magana kan kisan Kiristoci, Musulmai ma suna mutuwa a masallatai, kuma hakan na nuni da cewa rikicin Nijeriya ba na addini ba ne kaɗai, na rashin tsaro ne da rashin adalci.
A cewar rahoton, duk wanda aka kashe a wajen ibada, Kirista ko Musulmi, ya cancanci adalci da tausayi iri ɗaya.
