Trump ya jaddada barazanar kai wa Nijeriya hari yayin da Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zuwan Tinubu Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’amura na ƙara ɗaukar ɗumi tsakanin Nijeriya da Amurka bayan da Shugaba Donald Trump ya jaddada aniyarsa ta ɗaukar matakin soja akan Nijeriya bisa zargin kisan kiyashi ga al’ummar addinin Kiristanci.

Rahotanni sun bayyana cewa, Trump ya shaida wa manema labarai cewa yana duba yiwuwar ɗaukar matakin soja da suka haɗa da farmaki ta ƙasa da sama a matsayin wani ɓangare na shigar Amurka yaƙi da ta’addanci a Nijeriya.

A ƴan makonnin nan ne Trump ya sha maimaita zargin Gwamnatin Tarayya da gaza bai wa Kiristoci kariya, yana mai ikirarin cewa ana kashe su a gomman adadi da alwashin ba za su bar haka ya cigaba da faruwa ba.

Tun a ranar Asabar Shugaban Amurkan ya umarci jagorancin Pentagon da ya zana tsarin yaƙi, inda ya kuma yi gargaɗin matuƙar Nijeriya ba ta dakatar da haka ba, Amurka za ta kai mata hari.

Saidai, cikin hanzari Shugaba Bola Tinubu a wani rubutu ta kafa Soshiyal Mediya ya bada amsa ga ikirarin na Trump, inda ya ce Nijeriya ba ta taɓa tauye ƴancin wani addini ba.

Ya bayyana cewa, Nijeriya ƙasa ce da ke ƙoƙarin kare haƙƙin al’ummarta ba tare da la’akari da yanki ko addini ba, yana mai cewa dakarun tsaro suna iya ƙoƙarinsu wajen bai wa dukkan ƴan ƙasar kariya.

A wani labarin kuma, Fadar Shugaban Ƙasar ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Tinubu ya shirya tafiya Amurka domin ganawa da Trump, kamar yadda babban mai taimaka masa akan yaɗa labarai, Temitope Ajayi ya bayyana.

Ya kuma bayyana hakan a matsayin zance mara tushe ko asali da ake yaɗawa da nufin ruɗar da al’umma.

By Babaji