Jiragen ruwa 10 sun iso tashoshin Legas ɗauke da kaya daban-daban

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Aƙalla jiragen ruwa 10 ne suka iso manyan tashoshin jiragen ruwa na Lekki, Tin-Can da Apapa a jihar Legas, ɗauke da kayayyaki iri-iri da suka haɗa da takin zamani na urea, kwantena, man jiragen sama, dizel da kuma ɗanyen mai.

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta mai taken Shipping Position, wanda aka rabawa manema labarai a Legas ranar Juma’a.

Rahoton ya nuna cewa baya ga jiragen da suka iso, ana sa ran ƙarin jiragen ruwa 38 za su iso tashoshin Apapa, Lekki da Tin-Can Island tsakanin ranar 20 zuwa 28 ga Fabrairu. 

Waɗannan jirage ana sa ran za su kawo kayayyaki da suka haɗa da alkama, wake, ɗanyen mai, kwantena marasa kaya, takin urea, man jiragen sama, sinadarin haɗa mai (blended stock), simintin clinker, dizel, iskar gas da kuma sauran kayayyaki a cikin kwantena.

Hakazalika, rahoton ya ƙara da cewa akwai wasu jiragen ruwa 17 da tuni suke sauke kaya a tashoshin, ciki har da kwantena, ɗanyen mai, alkama, sukari, dizel, takin urea da kuma manyan motoci ɗaukar kaya.

Wannan yawan zirga-zirgar jiragen ruwa na nuna yadda harkokin shigo da kaya da man fetur ke ci gaba da ƙaruwa a manyan tashoshin ƙasar, musamman a birnin Legas wanda ke zama cibiyar kasuwanci da shigo da kaya mafi girma a Nijeriya.

Masana harkar tattalin arziki na ganin cewa ƙaruwar isowar jiragen ruwa na iya taimakawa wajen daidaita wadatar kayayyaki a kasuwa, musamman kayan abinci da makamashi.

Sai dai kuma, masu ruwa da tsaki a ɓangaren sufurin ruwa na jaddada buƙatar ƙara inganta ayyukan lodin da sauke kaya domin kauce wa cunkoso da jinkirin da ka iya haddasa ƙarin farashi ga ‘yan kasuwa da masu saye.

By ukarofi