Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jami’an tsaro da ke binciken zargin yunƙurin juyin mulki da aka so yi wa shugaba Tinubu sun gano mutane biyu waɗanda suka kashe kusan Naira miliyan 835 ta hannun kamfanoni biyu masu zaman kansu domin ɗaukar nauyin sojojin kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.
Ana zargin tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylɓa, da ba da gagarumar gudunmowa ta kusan Naira muliyan 785. Masu bincike kan lamarin sun yi zargin cewa an tura kuɗaɗen ne ta hannun kamfanin Purple Waɓes Limited, wanda kamfanin gine-gine da ke Abuja. Tuni aka kama sakataren kamfanin, John Ebokpo, kuma ana ci gaba da tsare shi.
Mista Sylɓa, ya riƙe mukamin ƙaramin ministan man fetur a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda shi ake zargi da zama babban mai ɗaukar nauyin masu shirya juyin mulkin.
Blueprint Manhaja tun da fari ta rawaito yadda ake zarginsa da hannu a yunƙurin juyin mulki, sai dai babu cikakken bayanin adadin kuɗin da ya bayar. Sai dai tsohon gwamnan ya musanta zargin sa hannu wajen kifar da gwamnatin Tinubu.
Har zuwa yanzu babu takamaiman yadda mista Sylɓa ke da alaƙa da Purple Waɓes Limited. Bayanan kamfanin a hukumar rajistar kamfanoni da kasuwanci (CAC) ba su ayyana shi a cikin daraktoci ko masu hannun jari ba a kamfanin ba. Kamfanin dai an yi masa rajista ne a watan Maris ɗin 2009 a matsayin kamfanin gine-gine.
Sai dai duk wani ƙoƙari na jin ta bakin Mista Sylɓa ta wayar tarho ya citura. Duk wani ƙoƙri da muka yi na mai magana da yawunsa, Julius Bokoru, da sauran daraktocin kamfanin Purple Waɓes Limited shi ma ya citura saboda lambobin wayoyinsu ba sa tafiya.
A lokacin da Premium Times ta kai ziyara ofishin kamfanin Purple Waɓes da ke Abuja a ranar Litinin, wani jami’in tsaro da ke aiki a wurin, ya shaida wa wakilinmu cewa an rufe ƙofar sama da wata 4 zuwa 5 — daidai da lokacin da aka kama dukkan waɗanda suke da hannu a yunƙurin juyin mulkin da aka so yi.
Mutum na biyu da ake zargi da ɗaukar nauyin juyin mulki shi ne Moses Zakwa. Ana zargin ya ba da gudunmowar Naira miliyan 50 ta hannun kamfanin Clay Ring Serɓices Limited, wani kamfani da ke jihar Legas kuma yana ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin. Kamfanin an yi masa rajista ne a matsayin mai gyare-gyare da kula da ayyuka.
Abin da aka sani game da mista Zakwa shi ne, a shekarar 2014 ya jagoranci zanga-zangar lumana a ƙarƙashin ƙungiyar matasa ta Kibaku a sakatariyar Alausa da ke Ikeja, inda yake neman a kuɓutar da yara ɗalibai ‘yan jihar Borno. Sai dai babu tabbacin cewa wanda ake tsare da shi a hannun jami’an tsaro shi ne ainihin mista Zakwa.
Jaridar Premium Times ta tuntuɓi daraktocin kamfanin Clay Ring Serɓices, sai dai ba mu iya samun su ta wayar tarho ba. Benjamin Okwumabua, ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin kamar yadda bayanan CAC suka tabbatar, amma kuma ba su da alaƙa da kamfanin.
A watan da ya gabata, shalkwatar tsaron Najeriya ta sanar da cewa ta kammala bincike har ma “ta tura wa mahukunta domin ɗaukar matakai”.
Rundunar sojin ta bayyana cewa bincikenta ya “gano wasu jami’ai da ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnati,” inda suka bayyana irin wannan yunƙuri da cewa, “ya saɓa wa ƙa’ida da ƙwarewa ta rundunar sojin Najeriya.”
Manhaja ta rawaito cewa an kama mutane 40 da ake zargi da suka haɗa da manyan jami’an soji a rundunar da ɗansanda da wasu fararen hula da ake zargi da hannun a wajen yunƙurin juyun mulki da shirya farfagandar juyin mulki.
Waɗanda ake zargi an kama su ne a wani samame bayan tattar bayanan sirri tsakanin rundunar sojin Najeriya da kuma ‘yan sandan farim kaya ta SSS.
Akwai kuma fararen hula da ake ci gaba da tsare su a hannun hukumar EFCC da SSS kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da samar da kayayyakin zirga-zirga da tsare-tsare. Wasu kuma an ba da belinsu.
Bincike ya nuna cewa manjo-janar mai ritaya na cikin manyan mutane da suke da hannu a wannan juyin mulki. Mista Adamu na cikin manya waɗanda ake zargi da Mista Sylɓa.
ɗaya daga cikin wanda ake zargi da hannu an gano cewa ya tsere zuwa Kudancin Amurka duk cewa hukumomi ba su bayyana haƙiƙanin wurin da yake zaune ba saboda dalilai na tsaro.
Manhaja a baya ta gano cewa masu shirya juyin mulkin so shiry akifar da gwamnatin Najeriya ne a lokacin da tsohon shugaban ƙasa Buhari ke miƙa mulki ga Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a lokacin rantsar da shugaban ƙasa.
Sai dai sun dakatar da shirin saboda matsalar ababen sufuri. Sai kuma a shekarar 2025 ne suka sake tada wannan shiri nasu bayan samun tallafin kuɗi daga mista Sylɓa.
Majiyoyi sun ce ana jiran umarnin shugaban ƙasa ne domin zartar wa da jami’an sojin hukunci a kotun sojoji.
Ana zargin Alhassan Maaji, wanda kanal ne mai lambar ɗaukar aiki N/10668 da shirya juyin mulkin da shirin kawar da wasu mutane a yayin kai farmakin juyin mulkin.
An dai shirya kawar da shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da manyan hafsoshin sojin Najeriya da kwamandojin burgediya da sauransu.
An sa wasu dakaru su ƙwace iko da fadar shugaban ƙasa da barikin Niger Barracks, da katafaren ginin rundunar sojin Najeriya (AFN) da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.
Masu binciken sun gano manyan bindigu da bindigun kakkaɓo jirgin sama da bindigogi samfurin PKT da AK-47 da bamabaman RPG da alburusai daga hannun AA Hayatu, wanda laftanar ne da ke bataliya ta 130.
Haka kuma an samu motocin Toyota Hiluɗ guda 4 da Toyota Prado SUɓ 1 da Toyota saloon cars 2, ɓolkswagen Golf guda 32 da ake amfani domin samamen ɓad da sahu.
