
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun da ta baza domin ƙaddamar da muhimman atisaye daban-daban a sassan ƙasar sun yi nasarar kama mutane 312 bisa zargin su da hannu a laifukan ta’addanci, sannan sun kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su guda 409 a watan Fabarairu.
Haka kuma, ta ce aƙalla mayaƙan ‘yan ta’adda guda 46 tare da iyalansu ne suka miƙa wuya.
Da yake zantawa da manema labarai akan ayyukan sojoji ranar Juma’a a Abuja, Daraktan harkokin yaɗa labaran DHQ, Manjo-Janar Michael Onoja ya ce sojojin sun kuma halaka ‘yan ta’adda da dama a watan Fabrairun.
Acewarsa, a yankin arewa maso gabas, dakarun atisayen Haɗin Kai sun ci galaba wajen kassara ayyukan ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP ta hanyar haɗin-gwiwa da jami’an haɗaka na hybrid forces, CJTF da kuma ‘yan sa-kai.
Ya bayyana cewa dakarunsu a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno sun daƙile wani mummunan harin wasu ‘yan ta’adda da suka yi yunƙurin kai farmaki ɗauke da wasu muggan makamai akan babura da tankunan yaƙi guda biyar, lamarin da ya yi sanadiyyar halaka da dama daga cikinsu tare da ƙwato makaman.
Haka ma a ranar 23 ga Fabrairun, inda sojoji suka karɓe wata mota ƙirar Toyota pick-up da aka cika ta da sassan ababen hawa, waɗanda aka yi yunƙurin safarar su ga mayaƙan Boko Haram tare da buhunan taki guda 460 a wani yanki na Ƙaramar Hukumar Bade da ke Jihar Yobe.
Ya ƙara da cewa, dakarun atisayen FANSAR YAMMA kuwa da ke aiki a shiyyar Arewa ta Yamma sun yi gagarumar nasara a yaƙi da ta’addanci a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Sakkwato da Zamfara.
A cewarsa, kutse cikin dazuka daga sojojin ƙasa da na sama da amfani da bayanan sirri ya taimaka wajen halaka ‘yan ta’adda da dama, inda kuma aka kama wasu 36 da ceto mutane 251 da aka sace.
Kazalika, ya ce ayyukan dakarun ya gudana ne a ranar 21 ga watan, inda suka ceto mutane 2q a ƙauyen Gidan Sarkin Bayero da ke Ƙaramar Hukumar Musawa a Katsina, waɗanda aka yi awon-gaba da su a ranar 19, sannan kuma tuni aka miƙa ga hukumomin gwamnatin jihar.
Sauran ayyukan dakarun a Jihar Filato ƙarƙashin sojojin ENDURING PEACE sun taimaka wajen daƙile ayyukan satar ɗan-adam ta’addanci da faɗan ƙabilanci a sassan jihar.
