
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun Ƙolin Nijeriya ta jaddada hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari ga Sanata Albaert Bassey bisa hannu a badaƙalar miliyan N240.
A wani zama na tawagar alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Stephen Jonah Adah, kotun ta tabbatar da hukuncin, wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a baya bisa samun sa da hannu a laifin.
Haka kuma kotun ta umarci a dawo da kuɗaɗen waɗanda adadinsu ya kai jimillar Naira miliyan 204 ga gwamnatin Jihar Akwa-Ibom.
A cewar Kotun Ƙolin, yayin da ta Ɗaukaka Ƙarar ta yanke hukuncin, ba ta bayyana ko za a dawo da kuɗaɗen ko kuma akasin haka ba, inda to ƙolin ta fayyace al’amarin.
An fara shari’ar Sanata Bassey me a lokacin da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta gabatar da ƙorafin badaƙalar akansa, inda aka gurfanar da shi a gaban Alƙali Agatha Okeke na Babbar Kotun Tarayya da ke Uyo a jihar ta Akwa-Ibom bisa tuhumar sa da laifuka bakwai da suka shafi rashawa da cin hanci.
EFC ta hannun lauyanta Ekele Iheanacho (SAN) ta zargi Bassey ne da karɓar cin hanci ta amfani da motoci 12 da jimillar kuɗaɗensu ta kai miliyan N254 a lokacin da yake kwamishinan kuɗi a Akwa-Ibom.
A ranar 1 ga Disambar 2022 kotun ta same shi da hannu a baki ɗaya laifuka bakwan, sannan ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai a kurkuku, wanda za su iya kaiwa 42 a gaba.
Bassey ya wakilci Akwa-Ibom ta Arewa maso Gabas a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2023. Sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi na jihar daga 2007 har zuwa 2014.
