
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta ce tallafin sojoji da gwamnatin Amurka ta kawo wa ƙasar ya samu ne ba tare da biyan wani farashi ba, sannan hakan bai rage darajar Nijeriya ba ko ta wace hanya.
Da yake ganawa da manema labarai a Abuja game da ayyukan dakarun a ranar Juma’a, Kakakin babban ofishin tsaron, Manjo Janar Michael Onoja ya ce tallafin na Amurka ya samu ne domin bai wa sojojin ƙarin ƙarin horo da ƙarfafa wa ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci, yana mai cewa hakan ba abu ne da za a riƙa yi wa kallon baƙon abu ba.
Ya ce, kare martabar Nijeriya da ba ta tsaro na nan daram, yana mai cewa babu wani sashe na martabar ƙasar da aka sauya da tallafin.
Manjo Janar Onoja ya kuma kirayi al’ummar Nijeriya da mayar da hankali akan darajar haɗakar da aka ƙara wa atisayen ƙasar a madadin adadin jami’an ƙasashen waje da ake damawa da su akan al’amarin.
A cewarsa, haɗakar a tsawon sama da watanni biyu da aka faro ta, ta samar da gagarumin sakamako na ci-gaba, sannan ana fatan samun ƙarin nasarori a kwanakin da ke tafe.
Daraktan watsa labaran hedikwatar ya kuma bayyana cewa, dakarun na Amurka a ƙasar suna gudanar da atisayen bayar da horo ga na Nijeriya, kamar yadda na Nijeriyar ke fita ƙasashen waje domin karɓar horon da ya shafi ƙwarewar ayyukansu.
Kazalika, ya ce jagororin sojoji a yankunan da ke fama da taɓarɓarewar tsaro suna cigaba da kula da halin da ake ciki tare da ƙoƙarin ɗaukar matakan daƙile hare-haren ‘yan ta’adda.
