Jiragen ruwa 18 ke sauke kayan fetur a tashoshin Legas – NPA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) ta bayyana cewa, jiragen ruwa 18 na sauke kayan man fetur da sauran kayayyaki a tashoshin Apapa, Lekki da Tin-Can da ke jihar Legas.

NPA ta bayyana cewa, jiragen na sauke takin zamani, sikari, man fetur da sauran muhimman kaya da kwantena.

Rahoton Kamfanin Labarai ta Nijeriya (NAN) ya nuna cewa, jiragen ruwa 46 masu ɗauke da man fetur, kayan abinci da sauran kaya ana sa ran isowar su tashoshin Legas tsakanin ranar Asabar zuwa 22 ga Fabrairu.

NPA ta ce, jiragen da ake sa ran isowa za su kawo kayan takin urea, alkama, kwantena marasa kaya, ɗanyen mai, gypsum, motoci, gas, kwantena na kayan daban-daban, gishiri da man fetur.

Haka kuma, an bayyana cewa jirage bakwai sun iso tashoshin kuma suna jiran samun wurin sauke kaya, ciki har da urea, ɗanyen mai, dizel, man jirgin sama da dai sauransu.

By ukarofi