Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun kama wani ɗan kasuwa ɗan asalin Nijeriya mazaunin ƙasar Chana tare da wasu ’yan ƙasar Angola biyu, bayan da suka fitar da jimillar ƙunshin hodar iblis 236 daga jikinsu, bayan gwajin da ya tabbatar da sun haɗiye miyagun ƙwayoyi a filayen jiragen sama na Abuja da Kano.
A wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ƙarshen mako, ya ce an kama Ibeanu Vincent Chukwudulue mai shekaru 34 a ranar Laraba 4 ga Fabrairu, 2026, yayin da yake ƙoƙarin hawa jirgin ƙatar Airways daga Kano zuwa Chana ta Abuja da Doha.
Sanarwar ta ce, jami’an NDLEA sun samu sahihan bayanan sirri, wanda ya sa suka dakatar da shi kafin tashinsa, tare da gudanar da gwajin na’urar duba ciki a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe. Gwajin ya tabbatar da cewa ya haɗiye miyagun ƙwayoyi.
An ajiye shi ƙarƙashin kulawa ta musamman, inda daga bisani ya fitar da ƙunshin52 na hodar iblis masu nauyin gram 735.95. A cewar NDLEA, wanda ake zargin ya bayyana cewa yana harkokin kasuwanci a tsibirin Legas kafin ya koma Guangzhou na ƙasar Chana a shekarar 2024.
A rana guda kuma, jami’an NDLEA sun kama wasu ‘yan ƙasar Angola biyu, Mbandu Martins Makiadi mai shekaru 50 da Ngoma Wilson Fernando mai shekaru 52, a ɗakin tashi na filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, yayin da suke ƙoƙarin tafiya da jirgin Ethiopian Airlines zuwa Istanbul ta Addis Ababa.
Binciken na’urar duba ciki ya kuma tabbatar da cewa su ma sun haɗiye miyagun ƙwayoyi. Daga bisani, an tsare su domin fitar da ƙunshin hodar iblis daga jikinsu a ƙarƙashin kulawar likitoci.
Hukumar NDLEA ta jaddada cewa za ta ci gaba da tsaurara matakai a dukkan filayen jiragen sama da kan iyakokin ƙasa domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi, tare da gargadin masu shiga irin wannan harka da su yi tunani sau biyu, domin dokar ƙasa ba za ta sassauta musu ba.
