Kwastom ta bayyana asalin farashin Dala a tsarin shigo da kaya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta fitar da cikakken bayani kan yadda ake amfani da farashin canjin kuɗin waje wajen kimanta kayayyakin shigo da fitarwa, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan wasu rahotanni kan farashin dala da ake amfani da shi a harkokin Kwastom.

A cikin sanarwar da Kakakin Hukumar, Abdullahi Maiwada, ya fitar a madadin Kwanturola-Janar na Kwastom, hukumar ta jaddada cewa ba ita ke ƙayyade ko sauya farashin canjin kuɗin waje da ake amfani da shi ba.

Ta bayyana cewa duk farashin da ake amfani da shi a tsarin ta na dijital mai suna B’Odogwu, wanda aka fi sani da Unified Customs Management System, ana aikowa da shi ne kai tsaye daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta intanet.

Hukumar ta bayyana cewa, CBN ita ce hukuma ta doka da ke da ikon ƙayyade farashin canjin kuɗi ƙarƙashin tsarin kuɗi na ƙasa. Don haka, NCS ba ta da ikon ƙirƙira, gyara ko ƙara wani kaso a kan farashin da ake amfani da shi wajen kimanta kaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, duk farashin da CBN ta aika ana shigar da shi kai tsaye cikin tsarin B’Odogwu ba tare da wani tsangwama ba, kuma ana amfani da shi a dukkan ofisoshin kwastom a faɗin ƙasa. Wannan tsari, a cewar hukumar, yana tabbatar da gaskiya, daidaito da kuma ingancin bincike.

Hukumar ta yi ƙarin haske cewa tsarin B’Odogwu yana aiki ne ta hanyar haɗin bayanai kai tsaye da CBN, inda yake karɓar sabbin farashi da zarar an turo su. Idan kuma aka samu tangarɗa na ɗan lokaci a hanyar isar da bayanai, tsarin zai ci gaba da amfani da farashin ƙarshe da CBN ya bayar har sai an sabunta shi, domin tabbatar da daidaito da ɗorewar aiki.

Dangane da rahoton da ya ambaci farashin N1,451.63 kan kowace dala a ranar 6 ga Fabrairu 2026, NCS ta bayyana cewa wannan adadi bai fito daga tsarin B’Odogwu ba.

Ta ce, an samo shi ne daga wata tsohuwar kafar bayanan kasuwanci wadda ba ta nuna bayanan kimanta kaya kai tsaye. Haka kuma, ta ce tsarin NICIS ba shi ne sahihin tsarin da ake amfani da shi wajen kimanta kaya kai tsaye ba.

Hukumar ta jaddada cewa sahihin farashin da aka yi amfani da shi a ranar 6 ga Fabrairu 2026 shi ne N1,365.56 kan kowace dala, kamar yadda CBN ta sanar a hukumance. Ta ce duk farashin da ake amfani da su bayan wannan suna bin sahihin bayanan da CBN ke aikowa kai tsaye, bisa tsarin manufofin kudi da haraji na ƙasa.

NCS ta sake tabbatar da ƙudurinta na tabbatar da gaskiya, daidaito da kuma sauƙaƙa kasuwanci ga masu shigo da kaya, masu fitar da kaya, dillalan kwastam da sauran abokan hulda na ƙasa da ƙasa. Ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin ta na dijital da inganta ayyuka domin tallafawa bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar gudanar da harkokin kwastom cikin kwarewa da riƙon amana.

A ƙarshe, hukumar ta bayyana cewa wannan ƙarin haske na da nufin wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa fahimta kan yadda tsarin farashin canjin kuɗi ke aiki a harkokin kasuwanci da tattalin arziki.

By ukarofi