
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Kakakin Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya yi watsi da ikirarin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan cewa ƙungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai shiga tsakani wajen tattaunawarta da Gwamnatin Tarayya.
A wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, Shehu ya bayyana kalaman Jonathan a matsayin ƙarya kuma abin ruɗarwa da ake ƙoƙarin siyasantarwa, yana mai cewa ba daidai ba ne ace tsohon shugaban ƙasar ya yi ƙoƙarin sake rubuta tarihi domin cimma wata manufar siyasa a zaɓen 2027.
A cewar Shehu, Muhammad Yusuf, wanda ya samar da Boko Haram ko magajinsa Abubakar Sheƙau ba su taɓa naɗa Buhari a irin wannan matsayin ba.
Saɓanin haka, ƙungiyar ta sha bayyana ƙin amincewa hakan da ma yunƙurin halaka Buhari, yana mai bada misali da harin Bomb da aka kai wa Buharin a 2014 lokacin da ya je yaƙin neman zaɓe a Jihar Kaduna, inda a nan wasu mataimakansa suka jikkata.
Al’amarin ya samo asali ne a tsakanin shekarun 2012 da 2013 da ɓangaren Boko Haram ta hannun wani Abu Mohammed Ibn Abdulaziz ya yi ikirarin cewa Buhari tare da wasu jagororin al’umma a Arewa irin su marigayi Shettima Ali Monguno da Ambasada Gaji Gatimari za su zama ƴan shiga tsakani a tattaunawar ƙungiyar da kuma Gwamnatin Tarayya.
Saidai, jam’iyyar Buhari ta CPC a lokacin ta yi sauri ta ƙaryata rahotannin da ke ƙoƙarin tabbatar da haka ta hannun Sakataren yaɗa labaranta, Injiniya Buba Galadima.
