Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Kwanturola mai kula da ofishin Jihar Kano na ma’aikatar ƙwadago ta tarayya, Alhaji Abdullahi Aliyu ya bayyana cewa lokaci zuwa lokaci suna shirya taro don ƙara bayyana irin yanayin ayyukansu ga ma’aikata na kamfanoni dama na gwamnatoci don ƙara fahimtar juna da dokoki don kyautata samun zaman lafiya tsakanin masu kamfani da ma’aikatansu.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron da suka gudanar da masu kamfanoni da ma’aikata a Kano ya bayyana cewa suna taron ne don tabbatar da masu kamfani suna bin doka da kula da rayuwar ma’aikata yadda ya kamata ta basu haƙƙoƙinsu su kuma ma’aikata ya zamana suna bin ƙa’idodi na aiki da yin abinda ya kamata, hakan shi zai haifar da zaman lafiya tsakaninsu.
Ya ƙara da cewa ita Gwamnatin Tarayya da duk wata hukuma ma, abinda tasa a gaba kafin komai shine zaman lafiya, wanda yana da muhimmanci kamfanoni da abokan hulɗa ma’aikata ya zamanto suna zaune lafiya shine zai kawo cigaba.
Ya yi nuni da cewa ba a hana ɗan Adam yin kuka ,illa dai duk yadda ka kai da ƙoƙarin yin gyara, wani wajen ma idon ka ba zai kai ba, balle ka gani ka yi wani abu, amma suna yin iya ƙoƙarinsu a hukumance su tabbatar haƙƙoƙin da Gwamnati ta ɗora musu sun bi waɗanda haƙƙi ke wuyansu suna faɗakar da su suna kuma bibiyar su tabbatar suna bin dokokin, suna nasara kan hakan tare da cigaba da tabbatar da ana bin dokakin.
Ya ce mahalarta taron sun haɗa da manajojin kamfanoni da ƙananan ma’aikata da matsakaita da manya ana haɗa su tare ne saboda in kana so ka tabbatar da nasarar abu ka haɗa kowa, shi ƙaramin ma’aikaci idan yana da ƙorafi wani lokaci yana neman inda zai faɗa ne, in ka yi nasarar haɗa shi da babban ma’aikaci in ya yi ƙorafi a inda yake ganin yana da damar yi ko baka gayawa babban ma’akacin ga ƙorafi ba, to wata dama ce da babban ma’aikaci zai san ashe wani abu yana faruwa, kuma su a wajen za suji, saboda wani loki ko da sun je “inspection “basa ganin matsala in ba an haɗu a irin wannan taro sun ji ba, sai su gaya musu ga abinda yake na doka da shi ma’aikaci bai sani ba akai.
Alhaji Abdullahi Aliyu ya ce yin wannan taron ana ilmantar da masu kamfani da ma’aikata da janyo hankulansu lallai su bi doka ta jan hankalinsu “persuasion” da shawarwari don a cimma nasara tare, duk mai kamfani idan ya kyautatawa ma’aikata tamkar kanshi ya kyautatawa, domin suma za su kyautata masa idan bai kyautata musu ba, illar da zata auku ga kamfanonin shima ba zai ji daɗinsa ba, suna ƙoƙarin kowane ɓangare su basu shawarwari da za su kyautatawa juna.
Ya ce irin wannan taro suna tattara matsaloli su rubuta rahoto su aika ma’aikatar ƙwadago domin a ɗauki mataki da za a sa a doka don kyautata tsarin tafiyar da harkar ƙwadago tsakanin kamfani da ma’aikata, taron kuma na haɗin gwiwa ne tsakanin su da kamfanoni.
Ana gabatar da taron ne don amfanar da su kamfanonin da masu aiki da ita gwamnati wanda ita ribarta ta ga ƙasa ta zauna lafiya da samun cigaba na tattalin arziƙi su kuma masu kamfani suna yi ne don riba don su taimakawa ƙasa ta cigaba a samar da aikin yi shi kuma ma’aikaci yana yine don shima ya anfanar da kansa da iyalinsa ya kyautatawa harkokin rayuwar sa.
Da yake ƙarin haske game da taron ɗaya da ga jami’an ma’aikatar kwadago ta tarayya .Murtala Haruna Abdullahi” mai kula da kamfanoni “factory inspector” ya ce suna shirya taron ne domin faɗakarwa, horarwa da ƙarawa juna sani ta yadda masu ɗaukar ma’aikata da ma’aikata musamman a masana’antu da sauran wuraren aiki za a wayar musu da kai kan yanda za su yi aiki tare da kyautatawa a tsakanin su kamar yanda doka ta tanada.
