Ƙungiyar haɗin kan Funtua ta bada tallafi ga mutanen da suka kuɓuta daga hannun yan bindiga

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar haɗin kan Funtua sun kai tallafin kuɗi ga mutanen da suka kuɓuta daga hannun yan bindiga a yankin.

Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya fitar da sanarwar haka,ya ce sun ziyarci waɗannan mutane a gidajen su.

Yawancin waɗannan mutane sun shaƙi iskar yanci ne bayan an biya kuɗin fansa.

Kwamred Suleiman ya bayyana cewa mutanen da suka kuɓuta sun sami tallafi daga dubu biyar har zuwa dubu ashirin kowane domin su toshe wata kafa.

Sai shugaban ƙungiyar yayi kira ga yan bindiga a yankin da su yi koyi da yan’uwan su na wasu ƙananan hukumomi da suka rungumi sulhu da alummar yankunan “kuwa Allah ku dawo ku rungumi sulhu da mutanen gari domin samun ɗorewar zaman lafiya da cigaba a yankin.

Haka kuma kwamred Suleiman ya yi kira da ƙananan hukumomin da suka gudanar da sulhu da yan bindiga su yi ƙoƙari duka ɓangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar da suka cimma domin Jihar Katsina ta cigaba.

Ya bayyana jin daɗin sa kan yadda al’amuran yau da kullum suka dawo sakamakon zaman sulhu da akayi a tsakanin shugabannin al’umma da yan bindiga a wasu ƙananan hukumomi.

Ƙungiyar ta kuma raba tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi musamman mata da ƙananan yara marasa lafiya a babban asibitin Funtua.

Kwamred Suleiman ya ce da yardar Allah ƙungiyar za ta cigaba da amfani da ɗan abinda ke aljihun ta wajen tallafawa mabuƙata a yankin Funtua da Jihar Katsina baki ɗaya.

By ukarofi