Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ana zargin wani ɗan sanda mai muƙamin Sufeto, Aminu Ibrahim, wanda ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano da harbe kan sa bisa kuskure yayin da ya ke bakin aiki a unguwar Hotoro da ke Kano.
Manhaja ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 5:40 na safe, lokacin da jami’in, wanda ke aiki a caji-ofis din Hotoro, ya shiga bandakin wani kamfani a nan Hotoron.
Majiyoyi sun ce Ibrahim ya harbi kansa a cikin bisa kuskure yayin da yake yunƙurin tsugunawa akan masai ita kuma bindigar ƙirar AK 47 na rataye a wuyansa.
“An gano bindigar, mai lamba GT 4177, da harsasai a cikin ta kuma tana cikin yanayi na harbi ga kuma harsashi guda da ya fado. An ƙirga harsasai 29 daga cikin 30 da aka ba shi tun farko,” inji wata majiya da ke da masaniya game da lamarin.
An garzaya da wanda abin ya faru da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda likitan da ke kan aiki ya tabbatar da rasuwarsa. An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawarwaki na asibitin domin binciken likita.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a da zarar an kammala.
