Tasirin shimfiɗa bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano ga yankin Arewa – Gwamnatin Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin shimfiɗa bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK Gas Pipeline) ya samu gagarumin ci gaba. Wannan aiki na daga cikin muhimman manyan ayyukan raya tattalin arziƙin ƙasa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin kawo sauyi a fannin samar da makamashi, ƙarfafa masana’antu da kuma farfaɗo da kamfanonin da suka daɗe da durƙushewa musamman a Arewa.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a ranar Litinin a cibiyar ’yan jarida ta ƙasa dake Abuja.

Aikin AKK Gas Pipeline wani babbar hanya ce ta iskar gas mai tsawon kusan kilomita 614 da za ta haɗa Ajaokuta a jihar Kogi da Kaduna da kuma Kano. An ƙaddamar da aikin ne a shekarar 2020 ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na (Gas Master Plan), wanda aka tsara domin amfani da iskar gas wajen samar da wutar lantarki, bunƙasa masana’antu da kuma rage dogaro da mai (petrol da dizal).

Aikin zai bai wa Nijeriya damar amfani da albarkatun iskar gas da take da shi a arewacin ƙasar domin inganta tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi ga dubban matasa, da kuma rage farashin samar da wutar lantarki. Har ila yau, ana sa ran cewa shimfiɗar bututun za ta taimaka wajen jawo hannun jari daga ƙasashen waje, musamman a fannoni irin su ƙarafa, sinadarai da masana’antar abinci.

Masana sun bayyana cewa AKK Gas Pipeline ba wai kawai zai zama wata hanya ce ta sauya fasalin tattalin arziƙin Nijeriya ba, har ila yau zai baiwa arewacin ƙasar damar shiga cikin tsarin zamani na masana’antu, wanda hakan zai rage matsalar rashin ayyukan yi da talauci a yankin.

Aikin shimfiɗa bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK) na ɗauke da manyan fa’idodi da tasiri musamman ga yankin Arewa. Ga wasu daga ciki:

1. ƙarfafa masana’antu da masana’antar ƙarfe:

Ana sa ran bututun zai samar da iskar gas ga manyan masana’antu a Kaduna da Kano, musamman masana’antar ƙarfe, sinadarai, da sarrafa abinci. Hakan zai farfaɗo da masana’antu da dama da suka durƙushe saboda tsadar makamashi.

2. ƙirƙirar ayyukan yi:

Gina bututun ya riga ya samar da dubban ayyukan wucin-gadi ga injiniyoyi, ma’aikatan gini, da masu jigila.

Bayan kammalawa, bututun zai buɗe ƙarin ayyuka ta hanyar bunƙasa masana’antu da harkokin kasuwanci.

3. Rage dogaro da man fetur da dizal:

Da zarar masana’antu da kamfanoni suka fara amfani da iskar gas maimakon dizal, farashin samarwa zai ragu, kuma hakan zai rage farashin kayayyaki ga jama’a.

4. Inganta samar da wutar lantarki:

Wuraren samar da lantarki za su iya amfani da gas ɗin domin haaka ƙarfin wuta a Arewa. Wannan zai rage matsalar ƙarancin wuta da ke janyo asara ga masana’antu da ’yan kasuwa.

5. ƙarfafa tattalin arziƙin Arewa:

AKK zai baiwa Arewa damar shiga cikin tsarin zamani na tattalin arziƙi mai dogaro da masana’antu maimakon noma kaɗai.

Har ila yau, zai taimaka wajen jawo hannun jari daga cikin gida da waje.

6. Inganta rayuwar jama’a:

Farfaɗowar masana’antu da ƙirƙirar ayyuka za su rage talauci da zaman banza a tsakanin matasa.

Wannan zai iya rage rikice-rikicen tsaro da rashin zaman lafiya da ake fama da shi a yankin.

A takaice, aikin shimfidabututun gas na AKK (Gas Pipeline) na ɗauke da babban fata ga Arewa: zai iya zama ginshiƙin farfaɗo da tattalin arziƙi, ƙarfafa masana’antu, da kuma rage dogaro da gwamnati wajen samar da ayyukan yi.

By ukarofi