Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar Talata ya raba wa matasa 5,380 tallafin kuɗi har Naira miliyan 807 domin tallafawa ananan kasuwancinsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa kowanne daga cikin matasan da aka zaƙulo daga ƙananan hukumomi 44 na jihar ya samu Naira 150,000.
A yayin shirin da aka gudanar a Kano, Yusuf ya bayyana cewa manufar bayar da kuɗin ita ce domin ƙarfafa dogaro da kai da bunƙasa tattalin arzikin matasa.
Gwamnan ya jaddada muhimmiyar rawar da matasa ke takawa wajen mulk da ci gaban tattalin arziki da kuma gina al’umma.
Ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa wannan tallafi zai taimaka wajen canza hankalin matasa daga neman aiki zuwa ƙirƙirar ayyukan yi.
Yusuf ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗorewar shirin ƙarfafa gwiwar matasa.
Ya shawarci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, tare da gudanar da kasuwancinsu cikin ladabi da hangen nesa na dogon lokaci.
Daya daga cikin wadanda suka amfana, Musa Tanko, ya bayyana shirin a matsayin mai sauya rayuwa, inda ya ce ya shirya fara kasuwanci na sayar da shayi da Indomie da kudin N150,000 da ya samu.
Wata kuma, Rabi Habu daga unguwar Yankaba a karamar hukumar Nasarawa, ta yaba wa gwamnan bisa yadda ya gane irin hazaƙar matasa tare da tallafa musu wajen fara ƙananan kasuwanci.
