Za a yi wa yara miliyan 7.8 allurar rigakafin baƙon-dauro da Shan-inna a Jihar Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Asusun Kula da Al’amurar Yara ƙanana na Majalisar ɗinkin Duniya UNICEF ta ce za ta yi wa yara miliyan 7.8 allurar rigakafin baƙon dauro nauyin ‘Rubella’ da cutar shan inna da za a fara ranar 6 ga Oktoba a jihar Kano.

Shugaban Asusun dake jihar Rahama Farah ta sanar da haka a zaman da ta yi da manema labarai a garin Kano ranar Litini.

Rahama ta ce an gudanar da taron ne domin wayar da kan manema labarai da ƙungiyoyin da suka haɗa ƙawance da su kan dalilin gudanar da allurar rigakafin wanda zai fara ranar 6 ga Oktoba 2025 zuwa 16 ga Fabrairu 2026.

Asusun za ga gudanar da allurar rigakafin tare da hadin gwiwar Hukumar NPHCDA, Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO, Gavi, Gidauniyar Gates, kungiyoyin Kare Haƙƙin dan Adam da gwamnatin jihar Kano.

“Jihar Kano na daga cikin jihohin 21 dake rukunin farko da za a fara gudanar da allurar rigakafin cututtukan a ƙasar nan da za a fara daga ranar 6 da 17 ga Oktoba.

Rahama ta ce a kwanakin baya gwamnatin jihar ta yi wa yara 345,000 ‘yan kasa da shekara biyar allurar rigakafi a kananan hukumomi 44 inda ta samu kashi 82% zuwa 98% na haɗin kan mutane.

“UNICEF tare da goyan bayan NPHCDA ta aika da mutum 3,347 ma’aikatan da za au gudanar da allurar rigakafin sannan da kwalabe miliyan 4.5 na maganin bOPV domin ganin an yi wa yara miliyan 3.9 ‘yan ƙasa da shekarar biyar rigakafi a jihar.

“Za Kuma a yi wa yara miliyan 7.8 daga wata 9 zuwa shekarar 14 allurar rigakafin baƙon dauro nauyin ‘Rubella’.

Bayan haka Rahama ta nuna damuwar kan yadda mutum uku suka kamu da cutar Shan inna nau’in ‘type 2 (cVPV2)’ a jihar inda a shekarar da ya gabata mutum 31 a kananan hukumomi 17 ne suka kamu da cutar.

“Kafin a shiga watan Disemba burin shine a daƙile yaɗuwar waɗannan cututtuka sannan hakan zai yiwu ne idan gwamnati ta mara wa shirin baya.

Rahama ta mika godiyarta ga shugabanin ƙananan hukumomi musamman yadda suka yi ƙoƙari wajen halartar zaman da suka yi wajen tattauna hanyoyin da suka fi dacewa wajen yi wa mutane allurar rigakafin.

Ta yi kira ga gidajen jaridu da su taimaka wajen wayar da kan mutane domin tabbatar da an yi wa duk yara allurar rigakafi a jihar.

Shugaban fannin daƙile yaɗuwar cututtuka na Asusun Ahmed Tijani ya ce wannan shine mafi girma cikin allurar rigakafin da aka gudanar a kasar nan da Kudu da Saharan Afrika inda burin shine yi wa akalla yara miliyan 106 allurar rigakafi.

Rigakafin da za a yi zai hada da na cututtukan bakon dauro nauyin ‘Rubella’ l, Hepatitis, HPV, Shan inna da Onchocerciasis.

Ya ce za a yi allurar rigakafi bakin dauro nauyin ‘Rubella’ ne saboda yadda wasu yaran ke kamuwa da baƙon dauro bayan sun yi allurar rigakafin cutar.

Kodinatan Hukumar NPHCDA na jihar Kano Maryam Umar ta yi kira ga gidajen jaridu da au zage damtse wajen wayar da kan mutane mahimmancin yi wa yara allurar rigakafi.

“Muna dogaro da ku domin wayar da kan mutane su amince da yi wa ‘ya’yansu allurar rigakafi.

By ukarofi