Daga USMAN KAROFI
Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya aike da bayani zuwa kotun Southwark Crown Court a ƙasar Ingila, inda ya kare tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, a shari’ar da ake yi mata. A cikin bayanin da aka karanta a gaban kotu, Jonathan ya ce ba sabon abu ba ne a biya wasu kuɗaɗe ta hannun ɓangare na uku domin tallafawa ministoci a tafiye-tafiyen aiki na ƙasashen waje.
Jonathan ya kuma bayyana cewa shi ne ya amince da amfani da jiragen sama masu zaman kansu da Diezani ta yi a wasu tafiye-tafiyenta lokacin da take minista tsakanin 2010 zuwa 2015. Ya ƙara da cewa duk wani tallafi ko kuɗi da aka kashe ta irin wannan hanya ana rubuta shi kuma ana mayar da kuɗin idan ya dace.
A gefe guda, Diezani na fuskantar tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi cin hanci tare da wasu mutane biyu, ciki har da wani ɗan kasuwar mai. Duk wanda ake tuhuma ya musanta zargin. Masu gabatar da ƙara sun zarge ta da karɓar rashawa kamar kayayyaki masu tsada da gidaje na alfarma daga wasu ‘yan kasuwar mai domin tasiri wajen bayar da kwangiloli, amma masu kare ta sun ce ba ta da cikakken iko kan bayar da irin waɗannan kwangiloli.
