Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Allah ya yi wa shahararren mawaƙi ɗan asalin jihar Katsina Alhaji Sarajo Mai Asharalle rasuwa.
Ya rasu a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina bayan yayi fama da rashin lafiya.
Marigayi Sirajo Mai Asharalle na ɗaya daga cikin mawaƙa da sukai fice tun kafin a kirkiro jihar Katsina.
Farfesa Aliyu Ƙankara masanin waƙoƙin marigayi Alhaji Mamman Shata ya bayyana mai Asharalle a matsayin amini kuma makusanci ga Alhaji Mamman Shata.
Marigayi Mai Asharalle na ɗaya daga cikin mawaƙa na farko daka fara tallata jamiyar PDP a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar’adua a Katsina.
