APC a Katsina ta bayar da tikiti ga waɗanda suka sauya sheka daga PDP

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta bai wa ‘yan majalisar wakilai uku tikitin tsayawa takara kai tsaye domin wa’adi na biyu, bayan sun sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar mai mulki a jihar. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin cika alƙawuran da jam’iyyar ta ɗauka ga mambobinta.

Haka kuma, jam’iyyar ta sauya Sanata Nasiru Sani Zango da wasu ‘yan majalisar wakilai guda bakwai, bisa zargin rashin samun goyon bayan al’ummomin mazaɓunsu. Waɗanda aka bai wa tikitin kai tsaye sun haɗa da Hon. Salisu Yusuf Majigiri mai wakiltar mazabar Mashi/Dutse, Hon. Abdullahi Balarabe Dabai mai wakiltar Bakori/Danja, da kuma Hon. Abubakar Aliyu Illiyasu na mazabar Batsari/Dan Musa/Safana.

Rahotanni sun nuna cewa waɗannan ‘yan majalisa uku sun samu nasara ne a ƙarƙashin PDP a wa’adinsu na farko, amma sakamakon burinsu na sake tsayawa takara a karo na biyu, suka sauya sheka zuwa APC watanni kaɗan da suka gabata. A gefe guda kuma, daga cikin waɗanda aka sauya akwai Sani Danlami na Katsina ta Tsakiya, Hon. Abubakar Yahaya Kusada na Ingawa/Kusada/Kankia, Hon. Aminu Jamo na Daura/Sandamu/Mai’adua, da Hon. Dalhatu Tafoki na Faskari/Sabuwa/Kankara.

By ukarofi