Majalisar Zartarwa ta amince da 112 matsayin layin ko-ta-kwana na ƙasa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) ta amince da amfani da lambar 112 a matsayin lambar ko ta kwana ta ƙasa a dukkan matakai da hukumomi. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa tsarin ɗaukar matakin gaggawa a Nijeriya tare da samar da haɗin kai da daidaito wajen mayar da martani ga matsalolin gaggawa.Rahotanni sun nuna cewa NEC ta kuma amince da kafa kwamitin aiwatarwa na haɗin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban, wanda ofishin mataimakin shugaban ƙasa da hukumar NCC za su jagoranta. An cimma wannan matsaya ne a taro na 157 na NEC wanda aka gudanar ta yanar gizo ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.Shettima ya bayyana cewa lambar 112 ta zama wajibi domin rage jinkiri da cikas na tsaiko, yana mai cewa a lokutan haɗari kamar gobara, hatsari, fashi, ko matsalar lafiya, abin da ‘yan ƙasa ke buƙata shi ne ɗauki na gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba. Ya ƙara da cewa dole ne a samar da tsari guda da jama’a za su dogara da shi domin ceton rayuka, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin dukkan matakan gwamnati wajen samar da sakamako mai amfani ga al’umma.

By ukarofi