Daga USMAN KAROFI
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace mutane takwas a ƙauyen Garin Idi da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sokoto, inda aka ce wasu daga cikin waɗanda aka sace na da alaƙa da mataimakin gwamnan jihar. Majiyoyin yankin sun bayyana cewa maharan sun isa ƙauyen ne da misalin karfe 1:00 na dare ɗauke da babura takwas, inda suka fara harbe-harbe tare da tilasta mazauna kauyen guduwa zuwa dazuka da sauran wuraren tsira.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun yi kusan sa’o’i biyu suna cin karensu babu babbaka a cikin al’umma ba tare da wata ɗaukin gaggawa daga jami’an tsaro ba. Wani mazaunin ƙauyen ya ce bai taba jin harbin bindiga mai tsanani kamar na wannan harin ba, yana mai cewa sun saba da irin wadannan hare-hare, duk da cewa babu wani taimako daga hukumomi. Wani majiyar kuma ya bayyana cewa da farko maharan sun tattara kusan mutane 30, mafi yawansu mata da yara, amma daga baya suka saki wasu suka tafi da mutane takwas kacal.
Daga cikin waɗanda aka sace akwai maza uku da mata biyar, ciki har da Hassana Adare Maifata, Rabi Alhaji Ishaqa, Kwamuso Umar, Yar’aji Garba, Kabiru Alkasim, Sani Mu’azu, Jadi Alkasim da wata mata da ake zargin ‘yar uwar mataimakin gwamnan ce ta ɓangaren uba. Rahotanni sun nuna cewa yawancin waɗanda aka sace ‘yan uwan mataimakin gwamnan ne. Haka kuma maharan sun kai farmaki wani wajen cajin waya inda suka kwashe sama da wayoyi 100, power bank da kuma naira dubu 40. Mazauna yankin sun roƙi gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
