JUSUN: Tattaunawa ce mafita, ba yajin aiki ba — Dan Marayan Judiciary

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Daya daga cikin masu neman kujerar Mataimakin Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan Shari’a ta ƙasa (JUSUN), reshen Jihar Kano, Said Idris Maiturare, wanda aka fi sani da “Dan Marayan Judiciary”, ya bayyana cewa tattaunawa ce hanya mafi dacewa wajen warware matsalolin ma’aikata, maimakon shiga yajin aiki.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a yammacin ranar Alhamis, inda ya ce idan aka ba shi dama, zai fifita tattaunawa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin nemo mafita mai ɗorewa ga matsalolin ma’aikata.

A cewarsa, “Ni a ra’ayina, duk lokacin da aka samu matsala, tattaunawa da hukumomi ita ce hanya mafi dacewa. Yajin aiki ba koyaushe yake zama mafita ba, domin yana jefa ma’aikata da al’umma cikin wahala.”

Ya ƙara da cewa ba ya son ganin ma’aikata ko wani ɗan Adam cikin ƙunci, wanda hakan ne ya sa ake masa laƙabi da Dan Marayan Judiciary.

Said Idris ya kuma bayyana cewa tun kafin ya shiga takarar, ya kasance memba a kwamitin tallafa wa marayu na ƙungiyar JUSUN, inda ya taka rawar gani wajen kare haƙƙinsu da kyautata musu.

“Na yi imani cewa an halicce ni ne domin taimakawa marayu da sauran jama’a. Ni ma na ɗanɗana rayuwar maraya, shi ya sa nake ƙoƙarin zama uba ga marayu a wannan lokaci,” in ji shi.

A ƙarshe, ya buƙaci ‘yan ƙungiyar su ba shi goyon baya, yana mai cewa za su ga sauyi mai ma’ana idan aka zaɓe shi.

“Duk wanda ya zaɓe ni, bai yi kuskure ba. Za mu kawo cigaba da kare martabar ma’aikatan shari’a. Ba za mu lamunci tozarta ma’aikata a kafafen yaɗa labarai ba bisa zarge-zargen da ba su tabbata ba,” inji shi.

By ukarofi